SAKAMAKON BINCIKE: Shin gaskiya ne an maka Babban Bishop Ogunyemi na darikar Angalika a kotu, saboda ya ce El-Rufai ba zai taba zama Shugaban Kasa ba?

0

Ranar 23 da 24 ga Agusta, wasu jaridu da suka hada da The Source, Daily Times da SaharaReporters suka buga labarin cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta maka Babban Bishop na Darikar Angalika na Zaria, Abiodun Ogunyemi kotu.

Sun ce an gurfanar da shi ne saboda wasu kalamai da yayi cikin Nuwamba 2019, inda ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ba zai taba zama Shugaban Kasa ba.

GASKIYAR MAGANA:

Ba gaskiya ba ne. Labarin da suka buga din ya na cike da rudu. Domin sakamakon binciken wannan jarida ya tabbatar cewa ba a gurfanar da bishop din ba.

ME JARIDU SUKA BUGA GAME DA BISHOP OGUNYEMI?

Ranar 23 Ga Agusta SaharaReporters ta buga wani labari kamar haka, “Gwamnatin Jihar Kaduna ta maka Bishop Ogunyemi kotu, saboda ya ce Gwamna El-Rufai ba zai taba yin shugabanci a Najeriya ba.’

Jaridar ta ce Ogunyemi ya yi wannan kakkausan kalami cikin watan Nuwamba, 2019 saboda haushin yadda ake ruguje coci-coci da dama a Jihar Kaduna.

Ita ma Daily Times ta buga irin wannan labari a rana daya da SaharaReporters.

Washe gari 24 Ga Nuwamba, The Source ita ma ta rubuta wannan labari mai cike da rudu da rashin tantance labarai.

Jaridun uku sun nuna cewa kamar ilhama ce ubangiji ya yi wa Bishop Ogunyemi, kan El-Rufai.

TANTANCE LABARI:

Lallai kuwa Bishop Ogunyemi ya yi wannan kalami a ranar 23 Ga Nuwamba, 2019, ya ce El-Rufai ba zai taba zama shugaban kasa ba, har abada.

Gaskiya ne kuma an kai Ogunyemi kara s gaban Mai Shari’a na Kotun Majistare a Kaduna, a ranar 4 Ga Agusta, aka sake komawa kotu a ranar 17 Ga Agusta. Daga nan aka dage sauraro zuwa ranar 28 Ga Oktoba, domin a bada sararin sasantawar bangarorin biyu a wajen kotu.

Amma kuma takardun bayanan da PREMIUM TIMES ta samu sun nuna ana ruhumar Ogunyemi da laifin bata suna da kuma watsa batanci da karairayi tare da yi wa mai karar barazana. Amma ba a maka Bishop din kotu saboda ya ce El-Rufai ba zai taba yin shugabanci ba a Najeriya, har abada.

Rahoton da ‘yan sanda suka gabatar a kotu, wato rahoton mai gabatar da kara (FIR) ya nuna ‘yan sanda sun zarci Bishop Ogunyemi da yin kalamin batunci a jaridar Punch ta ranar Lahadi, 15 Ga Disamba, 2019.

Sai Daily Sun ta 13 Ga Disamba, 2019 ta buga cewa:

– An gayyaci Bishop Ogunyemi zuwa Ofishin Gwamnan Kaduna, akan wani coci da aka rushe a Zaria, amma bai halarci taron ba.

– “Ranar da aka gayyaci Basaraken Adara zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna, a ranar ce aka tare shi a kan hanya, aka yi masa kisan-gilla a kan hanya.

– “Cewa Gwamna na matukar jin haushin sa da kuma haushin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), saboda surutan da aka rika yi kan rushe cocin Zaria.

– “Wai lokacin da Bishop Ogunyemi ya ki yarda ya fada tarkon gwamnatin Jihar Kaduna, ta hanyar kin amsa gayyata zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna, sai aka shirya wata ganawa da shi a Kano. Ya na kan hanyar Kano ce aka tare shi, aka tilasta shi ya bada hakuri, amma ya ce ba zai taba bada hakurin ba.

‘Yan sanda sun kammala bincike, suka ce Ogunyemi ya karya doka ta Sashe na 371, ta 373 da ta 377 ta Jihar Kaduna, ta 2017.

Ko a bayanin da Bishop ya yi ga ‘yan Sanda a ranar 27 Ga Janairu da 11 Ga Fabrairu, Bishop bai ce ana ci gaba da shari’ar ba, saboda ya ce El-Rufai ba zai taba yin shugaban kasa ba.

Ya ce ya yi hira da jaridun Punch da The Sun, amma bai yi maganar kisan Basaraken Adara da jaridun ba.

Cewa ya yi a cikin wata wasika da ya aike wa wasu shugabanni na coci-coci aka zakulo bayanan, bayan sun shiga soshiyal midiya, aka watsa.

Bishop Ogunyemi kuma ya na fuskantar shari’ar da wani Biship na Wusasa, Ali Buga Lamido kai shi.

An maka Ogunbiyi ne saboda ya yi zargin cewa Bishop Ali Buba dan keken asirin Musulmai ne, saboda Badukatani ne. Wai kamar yadda Musulman duniya suka wakilta Barack Obama ya rika nuna cewa shi kirusta ne, alhali wai musulmi ne.

A karshe dai abin da jaridun suka buga, ba gaskiya ba ne.

Share.

game da Author