Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa ta bayyana cewa ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta kamo maharan da suka kashe dakacen kauyen Odu Amos Obere ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Nansel Ramhan ya sahida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a garin Lafia cewa tuni jami’an ‘yan sanda suka fantsama don cafko wadannan mahara.
Maharan sun kashe basaraken ne a wani harin bazata da suka kai masa har fadar da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a.
Sai dai ko da jami’an tsaron suka isa fadar basaraken sun iske shi a kwanshe sannan kuma maharan sun arce.
“Basarake Obere ya rasu a asibiti duk da kokarin da likitoci suka yi na ceto ran sa.
A karshe Ramhan ya yi kira ga mutane da su hada kai da jami’an tsaro domin samun bayanai game da kisan sarki Obere.