Hukumar Kasafta wa Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi Kudaden Gudanar da Ayyuka ta Kasa (RMAFC) ta bayyana cewa an yi wa Asusun Tara Kudaden Shiga na Gwamnati yawa, wanda a karshen wata ta ke rarraba ribar fetur da kudaden harajin da ake tarawa ta na rabawa.
Hukumar ta ce an gi wa asusun yawa saboda gwamnatocin uku na tarayya, jihohi da kananan hukumomi duk a kan asusun suka dogara kacokan wajen samun kudade.
Shugaban RMAFC ne Elias Mbam ys bauyana haka yayinda ya karbi Rahoton Karfin Arziki ko Takaicin Kowace Jihar Najeriya (ASVI) daga hannun Babban Editan mujallar Economin Confidential, Yushau Shuaib, a ofishin sa, a Abuja.
Bayan ya yi wannan gargadin, Elias ya kuma yi kira ga jihohin kasar nan kakaf su kara bazama da sa himma wajen kirkiro hanyoyin da za su rika samun kudin shiga.
Wannan rahoto na shekara-shekara (ASVI) ya na zaburar da hukumar RMAFC wajen sa kaimi ga jihohi domin su kara fito da hanyoyin samun kudaden shiga a cikin jihohi, maimakon a ko hankici wata jiha za ta saya, sai ta jira kudi daga asusun gwamnatin tarayya.
“Wato na yi nazari na gane cewa rahotannin da mujallar Econonic Confidential ke bugawa sahihai ne daidai suke, kuma alkaluman kididdigar da mujallar ke wallafawa game da gejin tattalin arzikin kasar nan, daidai su ke, babu labarai na boge ko shaci-fadi.” Inji Elias.
Da ya ke magana yayin gabatar da rahoton, Babban Editan Economic Confidential, Yushau Shuaib, ya ce ASVI ta dora jihohin kasar nan arankatakaf a kan sikelin karfin tara kudaden shiga na gida a cikin kowace jiha, tare da auna shi da abin da kowace jiha ke karba daga gwamnatin tarayya a kowace shekara.
“Ba don rufin asirin kudaden da yawancin jihohi ke karba daga Asusun Gwamnatin Tarayya ba, to da ba za su iya rike kan su ba. Saboda kididdiga ta nuna wasu jihohin ma ko kashi 10% bisa 100% na abinda suke samu daga Tarayya, ba su iya tara su a harajin cikin jihar su.”
Duk da haka Sbuaib ya yaba wa wasu jihohin da ke dan cirzawa baya ga Lagos da Ogun.
Jihohi kamar Ribas, Kaduna, Enugu, Kwara da Zamfara duk kudaden su ya karu a cikin 2019, idan aka yi la’akari da wadanda suke tarawa a shekarun baya. Amma a yanzu sukan tara fiye da kashi 10%.
Jihohin da ba su iya ciyar da kan su saboda karancin kudaden shiga da dimbin bashin da tilas sai sun dogara da gwamnatin tarayya, sun hada da Katsina, Kebbi, Borno, Bayelsa da Taraba, wadanda ki ruwan ‘pure water’ mai sanyi za a saya, sai an jira kudi daga gwamnatin tarayya.
Discussion about this post