RIKICIN KUDANCIN KADUNA: Matasan Kudancin Kaduna sun yi Zanga-zanga a Kaduna

0

Gungun matasa yan asalin yankin kudancin Kaduna sun gudanar da zanga-zanga a garin Kaduna ranar Asabar.

Matasan sun fito ne domin nuna rashin jin dadinsu ga yadda kashe-kashe yaki ci yaki cinyewa a yankin kudancin Kaduna.

Sai dai wannan zanga zanag bai yi tasiri ba, domin jim kadan bayan sun fito sai jami’an tsaro suka fatattake, har suka yi kane wasu daga cikin su.

Daga baya an sake su bayan sun yi alkawarin ba za su cigaba da wannan zanga-zanga ba.

Jagoran wannan zanga-zanga Nasiru Jagaba ya bayyana cewa an shirya wannan zanga zanga ne domin su nu na fushin su ga yadda ake kashe mutanen yankin da gangar duk da cewa akwai jami’an tsaro a yankin.

” Idan dai ba wata manufa ce ake da ita a boye ba, yaya za a duk da daruruwan jami’an tsaro da aka girke a wannan yanki, kullum sai an kashe mutane.

Idan ba a manta ba Kwamandan rundunar sojjin dake aikin samar da Tsaro a wannan yanki, Kwamanda Okonkwo, ya shaida cewa babban matsalar da ake samu a wannan yanki shine ramuwar gayya.

Ya ce ” Matasan kataf sukan garzaya su aikata ta’asa akan abokan fadan su. Suma daga baya sai a garzayo a darkake su. A kullum muna kokarin ganin an kawo karshen wannan abu amma irin haka na kawo mana cikas.

” Yayi kira ga shugabannin al’umma da na garuruwan su da su taya gwamnati da jami’an tsaro wajen kawo karshen wannan rikice-rikice a yankin jihar.

Share.

game da Author