RASUWAR KASHAMU: Kashamu ya zizzille wa hukuncin duniya amma mutuwa ta dauke shi – Obasanjo

0

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa lallai mutuwa ta shiga gaban kowa. Obasanjo ya bayyana haka da yake mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigayi sanata Kashamu Buruji da ya rasu ranar Asabar a Legas.

Marigayi Kashamu Buruji na daga cikin wadanda gwamnatin Amurka ke nema ruwa a jallo kan zargin harkallar safarar miyagun kwayoyi da take masa.

Bayan ita kanta kasar akwai wasu harkalla masu dama da ake zargin Kashamu da hannu dumu-dumu a ciki a kasar nan.

“Kashamu ya rika yin amfani da tarin dukiyar sa da ya tara, yana murde shari’a yana samun dama a duk inda ya ke. Sai dai kuma karfin dukiya, Mulki, matsayi, Siyasa basu hana mutuwa a duk lokacin da ta yi Sallama.

” Ina yi masa fatan Allah yayi masa rahama ya sa Aljanna ta zamo makomar sa. Sannan kuma ina mika ta’aziyya ta ga Iyalan sa, Allah ya basu ikon hakurin jure wannan rashi, Amin.

Marigayi, Sanata Kashamu Biuruji yayi fice matuka a harkar siyasar Najeriya. Sun rika kai ruwa rana tsakanin sa ta tsohon shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo wanda daga jiha daya suka fito, wato jihar Ogun.

Kashamu ya rasu a wani Asibiti dake Legas, bayan yayi fama da cutar Korona da wasu cututtuka.

Share.

game da Author