Farfajiyar finafinai Hausa ta fada cikin jimamin rashin jaruma Fadila Mohammed da ta rsau ranar Asabar a Kaduna.
Fadila ta rasu bayan fama da tayi da rashin lafiya.
Jaruman Kannywood sun mika ta’aziyyar su ga iyaye da ƴan uwan jaruman sannan kuma sun rika bayyana yadda suka yi aiki da ita a lokacin da take raye.
Jarumai kamar su Ali Nuhu, Adam Zango, Ummah Shehu, Fati SU, Maryam Booth, Rahama Sadau duk sun yi mata addu’ar Allah ya ji kanta ya sa Aljannah ya zamo makomanta.