Basarake a masarautar Barno, Zanna Boguma, ya soki salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari musamman wajen samar da tsaro a yankin Arewacin Najeriya.
” Hare-haren Boko Haram a yankin Barno, garkuwa da mutane da ayyukan ta’addancin da suka ki ci suka ki cinyewa ne abin tashin hankali a gare mu yanzu.
Basaraken ya ce babban dalilin da yasa ‘yan arewa suka yi tururuwa wajen zaben Buhari shine don a gama da Boko Haram, ayyukan ta’addanci da kau da tsanannin talauci a tsakanin mutane. Amma abun ya gagara har yanzu.
” Eh, tabbas an nada ‘yan Arewa mukamai da dama amma mukaman su bai amfanar da yankin da komai ba. Wannan mukamai nasu bai hana kashekashen da Boko Haram ke yi ba, bai hana mahara su kai farmakin su duk inda suke so ba sannan bai hana yin garkuwa da mutane a Arewa ba, duk da ko ‘ Yan Arewa ne suka yi masa ambaliyar kuri’un da yake tunkaho da.
Hakazalika, basarake Bogumo, ya kara da cewa dattawan Arewa sun bada gudunmawar su wajen ganin Buhari ya samu duk irin goyon bayan da yake bukata domin samun nasara a zabukan da aka yi, kyma yayi nasara.
” Ina daga cikin dattawan da suka tafi har kasar Amurka domin tallata Buhari, mun gana da manyan jami’an gwamnatin Amurka sannan mun kuma bayyana musu manufofin sa da irin abubuwan da yake so ya yi idan ya yi nasara a zabukan a wancan lokaci. Yanzu shekara biyar kenan cur yana kan mulki amma babu abin da ya sauya daga tabargazar da ya yi gado daga mulkin baya.
Jaridar Arewa Agenda da ta buga wannan hira, ta ce, A karshe basaraken yayi kira ga gwamnatin tarayya da Buhari su yi amfani da damar da ya rage musu na shekaru 3 da suka rage domin kawo sauyi nagari a kasa Najeriya da tabbatar da an gama da wadannan ‘yan ta’adda da suka addabi mutanen Arewa.