An kashe akalla mutum 415 a kashe-kashe daban-daban a Najeriya cikin watan Yuli, kamar yadda wani rahoto da wata kungiya mai suna Nigeria Mourn ta wallafa.
Cikin Rahoton Tashe-tashen Hankula a Watan Yuli”, Nigeria Mourn, wadda aikin da ta sa gaba a kasar nan shi ne bibiya da kididdigar kashe-kashen gilla a fadin Najeriya, ta ce wannan adadi da ta lissafa, kididdiga ce ta jihohi 21 kadai daga jihohi 36 na kasar nan da Abuja.
Wannan kungiya ta kan binciki rahotannin da kafafen yada labarai sahihai suka buga, sai kuma bayanan da ta tattara daga bakin iyalai, ‘yan’uwa ko majibintan wadanda aka kashe da ba a buga rahotannin su a jaridu ba.
Rahoton baya-bayan nan da kungiyar ta buga sun nuna jihohin Barno, Kaduna da Katsina ne aka fi yi wa mutane kisan-gilla a Najeriya, a cikin watan Yuli.
Ga yadda rahoton ya lissafa yawan mutanen da aka kashe a jihohin 21 da ta kididdige:
Kaduna – 139
Barno – 113
Katsina – 80
Kogi – 17
Nasarawa – 13
Taraba – 10
Benuwai – 9
Ebonyi – 8
Zamfara – 7
Filato – 5
Edo – 2
Akwa Ibom – 2
Lagos – 2
Oyo -1
Ogun – 1
Bayelsa – 1
Delta -1
Kebbi – 1
Rahoton ya ce mutum 185 duk mahara da ‘yan bindiga ne suka kashe su. Yayin da Boko Haram suka kashe mutum 123.
Makiyaya masu dauke da manyan bindigogi sun kashe mutum 67, wasu 26 kuwa wurin rikicin kabilanci aka yi musu kisan-gilla.
An kashe mutum shida a rikicin tankiya, wasu shida kuma jami’an tsaro suka yi musu kisan gilla kafin a gurfanar da su kotu.
Akwai kuma mutum biyu da suka rasa rayukan su a hannun fadace-fadace na kungiyar asiri.
283 da aka kashe fararen hula ne, sai jami’an tsaro har 132 aka kashe.
Rahoton baya na wannan kungiya ya nuna an kashe mutum 731 a cikin watan Yuni, cikin watan Mayu kuwa an kashe mutum 356.
Yayin da ake ci gaba da yi wa jama’a kisan-gilla, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta amince ‘yan Najeriya su mallaki lasisin mallakar bindiga.
Dama kuma Sanata Kabiru Marafa ya taba yin irin wannan kira cikin 2018, a lokacin ya na Sanata mai wakiltar Zamfara.