26 ga watan takwas na shekarar Miladiyya ita ce ranar da aka ware domin yaran Hausa. Ba wai an ware ranar don tunawa da yaren ba ne, domin ba ɓataccen yare ko kuma yana gab da ɓata ba ne. An ware ranar ne musamman don tayar da duk wani bahaushe daga bacci, da kuma jawo duk wani bahaushe dake ƙoƙarin barin hanyar da kaka da kanni suka ɗora shi a kai dangane da abin da ya shafi al’ada.
Amma abin mamakin shi ne: Duk da irin ƙoƙari na masu kishin wannan babban yare na Afrika, hakan bai hana da yawa daga cikin Hausawan faɗawa tarkon da aka ɗana musu don illata yaren nasu ba. Kai ba iya Hausawa ba, kusan duk wani yare na Afirka na fuskantar wannan barazana.
In ka duba, abin zai baka mamaki matuƙa. Ka ƙare tunaninka da ƙyar ka samu Bahaushe uku a cikin ɗari da suke amfani da sunan Hausawa. Duk mafiya yawancin sunayen da muke amfani da su sunaye ne ko dai na Larabawa ko kuma na Indiyawa. Hasalima muna ganin kamar abin kashi ne mu saka wa ƴaƴanmu sunan Hausawa.
Bahaushe yana da suna kala-kala kuma masu daɗi, amma sha’awar al’adun wasu ta sa muna ƙyamatarsu. Meye laifinka in ka saka wa ɗanka suna irinsu Tanko, Haƙuri, Jatau, Mati, Taimako, Kykkyawa, Ɗantani, Ɗalliti, Maihaƙuri, Maiƙarfi da dai sauransu. Ko ka sakawa ƴarka suna irin su Ladi, Altine, Gambo, Godiya, Maikyau, Maihankali, Alheri da dai sauransu. Waɗannan duk sunaye ne da zamu iya sanyawa yaranmu. Kuma ma mafiya yawan sunayen da muke arowa ɗin ai suna da ma’ana a Hausa: mu yi amfani da na Hausan mana.
Abin mamaki wai yanzu idan ka ji suna irin na Hausawa, to in ka bincika, zaka samu ba Bahaushe bane. Idan ka ji suna irinsu Godiya, Kasuwa, Alheri dss, to mai sunan ba Bahaushe bane. To me yaren namu ya mana da har wasu suke sha’awarsa mu kuma muke ƙyamarsa.
Wani abin haushi da ya faru kwanan baya. Wai ɗan sarkin Hausawa ne bai san me ake nufi da kalmar ‘matasa’ ba. Kai! Wannan abin takaici da yawa yake. To in ba ka san ma’anar ‘matasa’ ba, me ka sani kenan? To menene yarenka? Na farko dai kana da matsala da Hausa. Na biyu kuma kai ba bature ba ne. Dan kuwa ko ka fi Mista Ƙyanƙyan iya turan ci, baza ka taɓa zama bature ba.
Akwai wani bodiyo ma da yake yawo. Ana nuna wasu yara wai ƴaƴan Hausawa ne amma basu iya Hausa ba. Lokacin da na ga bidiyon, na tausayawa yaran nan. Domin kuwa iyayensu sun zalunce su. Amma ba za su gane hakan ba sai sun girma sun samu hankalin kansu. Lokacin da za su nemi abin da zasu ƙira amatsayin yarensu ko al’adarsu su rasa. Kuma ba yare ko al’adar da suka sani sai na Bature. Su kuwa turawa in kana atishawa ABCD ta faɗo daga bakinka saboda iya turanci, matuƙar kai baƙi ne, ba ruwansu da kai. Domin a wurinsu kai ‘Negro’ ne, ma’ana baƙin da aka sayo kakanninsa a matsayin bayi. A wannan lokacin yaran zasu fara zargin mahaifan nasu.
Muna ji muna ganin yadda ake kashe baƙaƙen fata a ƙasashen turawa, amma maimakon mu dawo gida mu yi ƙoƙarin inganta namu ƙasashen da al’adunmu, mun nace da raɓan jikin mutanen da basa ƙaunarmu.
Haƙiƙa Bahaushe ya kamata ya hankalta ya san meye a gabansa, y kuma san cewa shima fa al’adunsa abin sha’awa ne a wurin wasu. Ba ƙauyanci bane don ka inganta al’adarka. Kare mutunci ne. Misali, idan ka ziyarci ɗaya daga cikin ƙasashen Turai, sannan ka sanya kwat da laktayin, wallahi wani ma dariya zai maka. Domin baza ka taɓa sakawa kamar yadda suke sawa ba. Yadda muke yiwa ƙauyawa idan shigo birni suna ƙoƙarin kwaikwayan mutanen birni, muma haka za a yi mana idan mun je ƙasashen Turai muna ƙoƙarin kwaikwayan al’adunsu. Amma idan namu muka nuna, zamu yi komai cikin ƙwarewa, kuma zamu burge su sosai.
Wata rana wani ya bani labari cewa, a wata ziyara da ya kai Turai. Farkon zuwansa kwat da laktayin yake sakawa. Sai da ya yi sati ko aboki bai yi ba. Amma ranar wata Juma’a da ya yi wankan jamfa, yake ce min abin ya bashi mamaki. Yadda ya ga mutane suke sha’awarsa.
Saboda haka akwai buƙatar Bahaushe ya kula da al’adunsa ya kuma mayar da hankali wajen ganin inganta su ta yadda zasu zama abin sha’awa.
Bello Ibrahim Gangare