Fitacce kuma shahararren dan kwallon Barcelona, Gerrad Pique, ya bayyana cewa wasan da suka buga na Champions League, ya yi matukar tada masa da hankali.
” Wannan wasa bai yi min dadi ba. Na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bane za a yi wa irin wannan ci.
” Ni da kai na zan iya hakura da ci gaba da bugawa kungiyar kwallon kafa idan za a dauko matasa masu jini a jika su bugawa kungiyar. Amma wannan cin mutunci har ina?
Haka shima shugaban kungiyar, Bautomeu ya shaida cewa za a ga sauye sauye da kungiyar za ta yi nan ba da dadewa. Daga nan sai ya roki gafara yan kallo da masoyan Barcelona kan wannan rashin mutunci da Bayern Su kayi wa kungiyar.
Idan ba a manta na a daren Juma’a ne Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zubda abin fadi da kunya a wannan kakar kwallon kafa na Nahiyar Turai inda Bayern Munich ta kasar Jamus ta ragargazata, tayi mata rugurugu da kwallaye dai-dai har 8 a ragara ta.
Wasan dai kamar Uba na ja wa dan sa kunne har ya fusa ya rika shashshauda masa bulala kafin makwabta su cece wannan da. A wannan karon lokaci ne ya ceci Barcelona a hannun Bayern domin badon lokaci ba da kwallayen sun wuce 10 a ragar Barcelona.
Fitaccen dan wasan duniya, wato Leo Messi sai ya zama a bin Kallo a wasan gashi dai yana buga wasa amma kamar ba ya cikin wannan wasa.
Kwallaye 10 aka ci a wasan, Bayern ta zura kwallaye 9 cikin 10 domin mai tsaron bayan ta David Alaba yayi kuskuren dirka wa golin su kwallo ta ko wuce sai cikin raga.
Abin yayi wa Barcelona dadi a wancan lokaci domin 1-1 kenan. Amma kuma ashe mai yaya ne har da jikoki wannan kwallo da Alaba ya ci, kai har da tattaba kunne.
Dan wasan Barcelona Coutinho wanda aka tura shi aro na kakan kwallo shekara daya, da aka ce wai an tura shi ne saboda babu wurin da zai iya bugawa a Barcelona duk sun fi kwarewa, sai gashi shine ya ci kwallaye biyu a wasan.
Discussion about this post