Jam’iyyar APC mai mulki ta maida wa PDP jam’iyyar adawa raddi cewa, karya PDP ke yi, da ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai tabuka komai ba sai kara jefa ‘yan Najeriya cikin kangin fatara da talauci.
PDP ta yi wa Shugaba Buhari kaca-kaca biyo bayan jawabin da ya yi wa iakadun kasashen da ke Najeriya cewa tsawon mulkin sa na shekaru biyar zuwa yanzu, ya yi matukar kokari wajen yaki da cin hanci, rashawa da kuma fitar da ‘yan Najeriya cikin kangin talauci.
Jim kadan bayan kammala bayanin Buhari ne sai jam’iyyar PDP ta maida masa raddi, ta bakin kakakin yada labaran ta, Kola Olagbondiyan.
Kakakin ya ce bai kamata kamar Buhari ya rika yaudarar jakadun kasashe ba, domin maimakon fitar da Najeriya da ga damuwar da suka yi wa jama’a alkawarin za su yi, mulkin Buhari kara jefa Najeriya cikin rijiyar kuncin fatara da talauci ya yi.
“Banda kunci da kangin talauci babu abin da mulkin Buhari ya tsinana wa ‘yan Najeriya, sai tulin alkawurran karairayi.
“Ko yaro na goye ya san a yanzu a kasar nan, abinci ya yi tsada. Fetur ya yi tsada, rayuwa ta yi kunci.
“A mulkin Buhari ‘yan Najeriya da dama zama cikin kasar nan ya gagare su. Sun gwammace su tafi Turai ta hanyar kasa da jirgin ruwa. Da yawa sun gwamnace su mutu a cikin Sahara ko cikin teku, bisa ga zama cikin rayuwar kunci a karkashin mulkin APC.” Inji kakakin PDP.
Kola ya ce ba gaskiya ba ne da Buhari ya ce wa jakadun ya yi kokari wajen yaki da rashin tsaro, rashawa da kuma kawo yalwa a cikin kasa.
“Yau wace yalwa mulkin Buhari ya kawo? Duk abin da Buhari ya samu, zuwa yanzu kudin sa ya rubanya. Harkar tsaro kuma kowa ya san kara tabarbarewa ta yi. Da ya ce ya yi kokari a yaki da rashawa kuwa, wannan kowa ya san abin dariya ne kawai.”
Buhari ya shaida wa jakadun cewa ya yi nasara, duk kuwa da dimbin rikice-rikice da rigingimun satar bilyoyin kudaden da ake zargin makusantan Buhari. Da yawan harkallar kudaden kuwa an damfare su a kotu, ko maganar ba a yi.
Sai dai kuma APC ta ce mulkin Buhari ya ceto ‘yan Najeriya daga hannun kurayen PDP, wadanda suka bata shekaru 16 su na jidar kudaden kasar nan.
“PDP ba ta bar komai ba sai ayyukan da ta fara ta watsar bayan an biya kudaden. Sai kuma tulin kudaden Najeriya da shugabannin mulki a lokacin suka jide karkaf.”
A yanzu dai ‘yan Najeriya na kukan tsadar rayuwa, musamman tsadar abinci, inda da yawa ke cewa farashin abinci ya rubanya, sabanin yadda ya ke a lokacin mulkin PDP.