Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami, ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasika, cike da bayanan cewa shi ba barawo ba ne, kuma bai ma taba satar ko sisin-kwabo na gwamnati ba.
Ba a nan Malami ya tsaya ba, ya kuma lissafa wa Buhari dukkan kadarorin da ya mallaka tun kafin a nada shi Ministan Shari’a a 2015 zuwa yau.
Minista Malami ya rubuta wa Buhari wasika ce saboda matsin-lambar da kungiyoyin kare rajin dimokradiyya ke yi cewa a tsige Malami dangane da zarge-zargen wawurar kudade da jama’a ke yi masa, da kuma rubutattun raddin da tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu ya yi cewa Malami ya rika yi wa shirin yaki da cin hanci da rashawa zagon-kasa, tarnaki, dabaibayi da kuma zagon-kasa.
Wata kungiya mai suna Kanuri Collective Initiative, ta rubuta wa Buhari wasika, ta na neman a cire Malami saboda zarge-zargen da ake yi masa.
Kungiyar ta ce mutum kamar Malami, bai kamata a ce shi ne ministan harkokin shari’a ba.
Daya daga cikin Kwamitin Yaki da Cin Rashawa na Shugaban Kasa, Femi Odekunle, ya nuna cewa abin da ke faruwa tsakanin Magu da Malami, duk kwaryar sama ce ke dukan ta kasa.
‘Babu Guntun Kashi A Jiki Na’ -Malami
Malami ya shaida wa Buhari a cikin wasika cewa lokacin da aka nada shi minista a 2015, ya bayyana yawan kadarorin sa ga Hukumar CCB.
“Haka kuma ni na fara bayyana yawan kadarori na a ranar 2 Ga Yuli, 2019, bayan an sake nada mu.
“Ran Ka ya Dade, na ga ya dace na rubuto wannan wasika domin na shaida maka cewa ni ba barawo ba ne. Wasu magauta ne ke neman bata min suna. Amma na gama shirin maka su kotu, domin amsa tuhumar kazafi, sharri da bata suna da suka yi min.
“Babu wani abu da na ke yi a boye. Ni ina harkokin kasuwanci kafin a nada ni minista. Sannan na shafe shekaru 20 ina aikin lauya, a ciki na yi shekaru 7 a matsayin babban lauya (SAN).
“Na mallaki babban otel din Rayhaan da Rayhaan Food and Drinks a Kano. Kuma wadannan kadarori su na cikin kadarori 27 da na lissafa wa CCB cewa na mallaka.”
Malami ya hada da sunayen dukkan kadarorin sa, inda suke da kuma asusun ajiyar banki na kowane irin kasuwanci da ya ke yi, wanda ya ce kuma ya tsame hannun sa daga sha’anin kasuwsncin tun bayan nada shi minista da aka yi.