Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya soki hukuncin da shugabannin kungiyar Lauyoyi ta kasa suka yanke na soke gayyatar da suka yi wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai na halartar taron su na shekara-shekara bisa wasu korafe-korafe da basu tabbatar da gaskiyar su ba.
Sanusi Lamido ya ziyarci Kaduna domin halartar wasu tarorruka na wasu hukumomin jihar da gwamnan El-Rufaiya nada shi a jihar wanda ya hada da jami’ar Jihar Kaduna KASU.
Sanusi ya samu tarba mai matukar kyau domin tundaga tashar jirgin saman Kaduna daruruwan mutane suka yi cincirindo suna yi masa lale marhaban da zuwa birnin Kaduna garin gwamna.
A tattaunawa da yayi a ofishin gwamna El-Rufai Sanusi yayi tsokaci game da rashin jituwa da aka samu tsakanin gwamnan jihar da kungiyar Lauyoyi ta kasa wanda bayan ta gayyace shi taron kungiyar na shekara-shekara sai kuma ta soke bayan wasu tsiraru sun ce basu amince ya halarci taron ba.
” Ba zai yiwu ace wai shikenan daga wasu sun yi korafi akan mutum batare da an bashi dama ya wanke kan sa ba sai kungiya kamar ta lauyoyi ta yanke hukunci kai tsaye ba tare da tayi la’akari da abinda zai biyo baya ba.
” Idan da gaske ne akwai dalilin da ya sa suka janye gayyatar da suka yi masa, a ganina ai halartar sa ne zai basu daman su tambayeshi abinda ya shige musu duhu, yayi musu bayani dalla-dalla ba biye wa tatsuniyoyi kawai don wasu basu gamsu da jarumtar sa ba.