NAZARI: Abubuwan da ka iya biyowa baya, dangane da tulin basussukan da Najeriya ke ciwowa daga Chana

0

Yayin da ‘yan Najeriya ke bayyana damuwa da yawan tulin basussukan da Najeriya ke ciwowa daga kasar Chana, shi kuma Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, rokon ‘Yan Majalisar Dattawa ya yi cewa idan suka cika bin diddigin abin da aka yi ko yadda aka kashe kudaden, to masu zuba jari za su ji tsoron yin hulda da Najeriya.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin kawo wa masu karatu duk wani tarko, kujiya ko fatsar da ake tsoron za su iya zama tarnaki da dabaibayi ko karfen-kafa ga Najeriya nan gaba.

1. Shin Har Nawa Ne Adadin Kudaden Da Najeriya Ta Ciwo Bashi Daga Chana?

Amsa: Kididdiga daga Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO), ta nuna cewa daga 2010 zuwa 31 Ga Maris, 2020, an ciwo bashi sau 11 daga kasar Chana, kuma duk daga Exim Bank.

Dukkan basussukan dai sai bayan shekaru bakwai za a fara biyan duk wanda aka ciwo, kamar yadda ya ke a cikin yarjejeniyar karbar bashin. Kuma za a kammala biya cikin shekaru 20. Akwai kudin ruwa kashi 2.5 bisa 100 na yawan kudin da za a dora a kai.

2. Wadanne Ayyuka Aka Ce Za A Yi Da Kudaden?

Ayyukan da aka ciwo wa basussukan sun hada da Shirin Ayyukan Samar da Tsaron Najeriya ta Hanyar Tsarin Sadarwa, Shirin Zamanantar Tashoshin Jiragen Kasa na Idu zuwa Kaduna, Karamar Tashar Jirgin Kasa ta Abuja, Shirin Inganta ICT a Najeriya, sai kuma Shirin Fadada Tashoshin Jiragen Sama Hudu (Abuja, Kano, Legas da Fatakwal).

Sauran ayyukan sun hada da Aikin Tashar Lantarki ta Zungeru, Gina Masana’antun Casar Shinkafa 40, Aikin Zamanantar da Titin Jirgin Kasa na Lagos zuwa Ibadan, Gyaran Titin Abuja zuwa Keffi zuwa Makurdi, Gina Tashar Kera Kayan Gyaran Jiragen Kasa a Abuja da kuma Aikin Samar da Ruwan Sha a Abuja.

Bayanai sun nuna an ciwo bashin Aikin Inganta Tsaro ta Hanyar Sadarwa na Dala Milyan 399 da na Aikin Hanyar Jirgin Kasa daga Kaduna zuwa Abuja na Dala Milyan 500 tun cikin Disamba, 2010. Sai a 2030 za a kammala biyan sa.

Tuni an karbi kudaden, har an fara biya, saura Dala Milyan 322 da kuma Dala Milyan 403.

An karbo bashin Aikin Karamar Tashar Jirgin Kasa ta Abuja na Dala Milyan 500 da na Fasahar Zamani, ICT na Dala Milyan 100 a cikin Nuwamba, 2012 da Janairu 2013. Kuma an kashe kudaden a wurin ayyukan.

An fara biyan basussukan, amma akwai saura Dala Milyan 480 da kuma Dala Milyan 100 su ma da ba a kai ga kammala biya ba.

Ana bin Najeriya bashin Aikin Fadada Filayen Jiragen saman Abuja, Kano, Lagos da Fatakwal na Dala Milyan 500, Aikin Tashar Lantarki ta Zungeru Dala Milyan 984, Aikin Masana’antun Casar Shinkafa 40 Dala Milyan 325. Su kuma wadannan tilas a kammala biyan su cikin 2034, 2033 da 2036.

Aikin Titin Jirgin Kasa na Lagos zuwa Ibadan na Dala Bilyan 1.267, na Dala Milyan 460 don Gyaran Titin Abuja zuwa Keffi zuwa Makurdi, na Kayan Aikin Jiragen Kasa na Abuja na Dala Milyan 157 da kuma Aikin Samar da Ruwa a Abuja, na Dala Milyan 381, duk a cikin Agusta 2017 da Mayu, 2018 aka ciwo su.

Kenan za a kammala biya tilas cikin 2037 da 2028.

Ya zuwa Maris 2020, aikin Titin Jirgin Kasa na Lagos zuwa Ibadan ya lashe kashi 60 bisa 100 na bsshin, shi kuma Aikin Gyaran Titin Abuja zuwa Keffi zuwa Makurdi ya lashe kashi 17 bisa 100 kacal.

Me Ya Sa Gwamnati Ke Hakilon Kara Ciwo Wani Bashin?

A yanzu Najeriya na gaganiyar kasa ciwo bashin daga Chana domin gyara titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

To Me Doka Ta Ce Dangane Da Ciwo Basussukan?

Sashe na 41, 1(a) na Dokar Hakkin Kashe Kudade (FRA) ya ce duk bashin da za a ciwo, to a tabbatar ayyukan raya kasa za a yi da su.

Sannan kuma kada a ciwo bashin da zai yi wa ruwan cikin Najeriya nauyin dauka, har cikin ya kumbura, bashin ya zama alakakai.

Dokar kuma ta ce a ta tabbatar wajen bada kwangilar an karbi ‘tanda-tanda’ daga ‘yan kwangila daban-daban, yadda za a bada kwangilar ga kamfanin da ya fi cajar mafi kankantar kudin aiki.

Bincike ya nuna yawancin basukan ba kan ka’idar da ta dace aka karbo su ba, shi ya sa suke da wahalar biya.

Ba a bin dokar tsarin bayar da kwangila ballantana a san ta hanyar da ake bi a yi tunanin karba ko bukatar gudanar da ayyukan da kan haifar da ciwo bashi a bisa tilas. Majalisar Zartaswa ce kadai ke kidan ta, kuma ta yi rawar ta.

‘Yan Najeriya ba su ganin taswirar aikin da za a gudanar.

Ba kamar basussukan Bankin Duniya ko Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) da sauran bankunan Turai masu shata komai dalla-dalla ba tare da nuku-nuku ba, shi bashin Chana ba a taba baje shi a faifai ‘yan Najeriya sun ga ‘kabali’ da ‘ba’adin’ da ke cikin sa ba.

Tankiya guda biyu kadai da ke cikin Dokar Hakkin Kashe Kudade (FRA) da Dakar Sharuddan Bayar da Kwangila sun sa dukkan basussukan da ake karbowa daga Chana, haramtattu ne, kai ko da Majalisar Tarayya ta rattaba hannun amincewa a karbo basussukan.

Duk wata gwamnatin da ta san abin da ta ke yi idan ta hau mulki nan gaba, za ta iya soke kwangilar, ta ce ba ta biyan sauran bashin, domin a cikin duhu aka yi cinikin aka taya, aka sallama kafin haske ya bayyana har a ga ko su wane ne dillalan.

Shin Bashin Chana Abin Damuwa Ne?

Kwarai kuwa abin damuwa ne, domin Chana ta yi kaurin suna wajen yi wa kasashe ‘yar-burum-burum ko shigo-shigo-ba-zurfi. Sai an shiga ruwa ya yi awon gaba da mai tsautsayi ko ganganci. Ta yi wa Sri-Lanka da Ethiopia da wasu kasashe da dama haka, wadanda a karshe sai dai suka mika wa Chana saniyar da suke tatsa sukutum. Ita kuma Chana ta rika tatsa, kuma duk la’ada a ciki.

Share.

game da Author