Gwamnatin kasar Ireland ta rattaba hannun amincewa za ta maido wa Najeriya wasu fam milyan 5.5 da tsohon shugaban mulkin soja, marigayi Sani Abacha ya zace ya boye a wani asusun kasar.
Ministar Shari’a ta Ireland, Helen McEntee ce ta bayyana haka, tare da karin bayanin cewa tun cikin 2015 kotun kasar ta kwace kudaden, ta hana a taba su.
McEntee ta kuma an kwace dukiyar a wani banki ne da ke Dublin, babban birnin kasar, a cikin 2014, gagarimin aikin da ta ce Hukumar Dakile Rashawa ta kasar ce ta kwace makudan kudaden.
Hakan inji ta ya faru ne bayan da wakilan tawagar wasu lauyoyi daga Najeriya sun tuntubi kasar dangane da kudaden wadanda aka sato din daga Nijeriya zuwa Ireland.
“Ina mai matukar murna da farin cikin sa wa wannan yarjejeniya hannu da wakilan gwamnatin Najeriya.” Haka Ministar ta bayyana a shafin ta a gwamnatin kasar.
Ta ce an dade ana kwan-gaba-kwan-baya a kan kudaden, wadanda aka kwace din kimanin daka bilyan 1, wadanda aka tabbatar da kimshe fam milyan 5.5 a wani bankin Ireland.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Ministan Shari’a na kasar ya bayyana cewa an karbo dala milyan 311 daga Asusun Amurka da na Tsibirin Jersey.
Cikin 2016 Shugaba Muhammdu Buhari a zangon sa na farko ya taba cewa Abacha ba barawo ba ne.