Najeriya ta ɗage ranar sake buɗe zirga-zirgar jiragen sama sauka da tashi daga kasashe

0

Najeriya ta bayyana cewa ta dage ranar fara tashi da saukar jiragen sama daga ranar 29 Ga Agusta zuwa ranar 5 Ga Satumba.

Tun farko dai Najeriya ta tsara cewa jiragen sama za su fara tashi da kuma sauka Najeriya ne daga ranar 29 Ga Agusta.

Sai dai kuma wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta fitar, ta ce an dage ranar fara zirga-zirgar zuwa ranar 5 Ga Satumba.

Ba a bayyana dalilin dage ranar ba a cikin sanarwar da Ma’aikatar ta fitar a shafin ta na Twitter ranar Alhamis.

Farkon makon nan PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cewa za a fara zirga-zirgar a ranar 29 Ga Agusta, kuma an buga sabbin sharudda da ka’idojin da Gwamnatin Tarayya ta nemi duk wani bako ko fasinja daga kasashen waje zai cike, kafin a bar shi ya sauka ko ya shiga cikin kasar nan, bayan saukar a filin jirgi.

Najeriya za ta ci tarar jirgin saman da ya shigo da wanda ba ya da takardar shaidar gwajin-cutar-Korona.

Kodinetan Kwamitin Shugaban Kasa na Dakile Cutar Coronavirus, Sani Aliyu, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta bar wani dan kasar waje shigowa ba, har sai ya nuna shaidar cewa an yi masa gwaji a kasar sa cewa ba shi dauke da cutar Coronavirus.

Aliyu ya yi wannan jawabi a wurin taron ganawa da manema labarai na Kwamitin Shugaban Kasa mai Dakile Cutar Coronavirus.

An gudanar da taron da manema labarai ne a Abuja a ranar Litinin din nan.

Da ya ke karin bayani kan sabbin ka’idojin da gwamantin Tarayya ta gindaya dangane da bude filayen jirage da za a yi a fara shigowa da fita Najeriya daga ranar 29 Ga Agusta, Aliyu ya ce duk wani fasinjan da zai shigo Najeriya, tilas sai ya nuna takardar shaidar an yi masa gwajin cutar Coronavirus akalla mako guda, wato kwanaki bskwai da yin gwajin, kafin ya shigo Najeriya tukunna.

‘Duk Wanda Ya Shigo Najeriya Sai Mun Killace Shi Sati Daya’:

Akiyu ya kara da cewa duk wani fasinjan da ya sauka filin jirgin Najeriya, to kafin a bar shi ya shiga gari, sai an killace shi tsawon kwanaki 7 tukunna. Dama kuma sai an gamsu da takardar shaidar ba shi dauke da cutar Coronavirus tukunna kafin ma a bar shi ya fita daga filin jirgin.

Abin Damuwa: Game da damuwar da ake nunawa cewa sai mai dauke da katin shaidar rashin cutar Coronavirus a jikin sa za a bari ya shigo Najeriya, Aliyu ya ce za a duba lamarin a lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya ce jami’an lafiya ne za su rika kuka da fasinjonin da za a killace. Kuma duk bakon fasinjan da ya ki bari a yi masa gwaji, to za a hada shi da jamii shige-da-fice domin su dauki matakin da ya dace a kan sa.

Rahotanni sun ce Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ya ce Najeriya za ta hana duk wani jirgi sauka, muddin kasar sa ta hana jiragen da suka tashi daga Najeriya sauka a cikin kasar.

Sirika ya ce an yi taro an sanar wa masu kamfanonin sufurin jirage wannan ka’ida.

“Akalla fasinjoji 1,280 za su rika sauka Najeriya a kullum daga kasashen waje, a filayen jiragen Lagos da Abuja.”

Share.

game da Author