Najeriya ta aika wa gwamnati da mahukuntan ƙasar Ghana da saƙon jan kunne cewa lallai su shiga taitayin su tunda wuri domin kuwa muzgunawa ƴan Najeriya da ƙasar ke yi ya kai maƙura yanzu.
Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed ya fitar da wannan sako inda ya umarci ƙasar Ghana ta bude kunnuwarta ta saurari wannan gargaɗi.
A shimfiɗaɗɗiyar sanarwar da Lai Mohammed ya fitar ranar Juma’a, ya ce yanzu ya kai ga gwamnatin Ghana har kwace ofishin jakadancin Najeriya tayi dake titin Barnes dake babban birnin kasar, Accra da ƙarfin tsiya sannan kuma ta sake zuwa ta rusa wani gini mallakin gwamnatin Najeriya dake titin Julius Nyerere a ƙasar.
” Bayan haka, shekaru uku kenan duk shekara sai ƙasar ta dawo da daruruwan ƴan Najeriya gida wai basu takardun zama a ƙasar da ko kuma basu shiga ƙasar bisa ƙa’ida ba.
” Sannan kuma mahukunta a ƙasar na bi suna garƙame shagunan ƴan Najeriya babu gaira babu dalili, bayan ta zabga musu kuɗin haraji.
Kuma gwamnatin ta yi wa dokokin zaman kasar garambawul da yanzu ta tsawwala kudin sabunta lasisin zama a Ƙasar duk shekara wanda a Najeriya dan ƙasar Ghana naira 7000 kacal yake biya kuɗin zaman ƙasar.
Haka kuma da gangar mahukuntar kasar suke tsananta shari’a akan ƴan Najeriyan da ya fada hannun su. Zuwa yanzu akalla mutum 200 ƴan Najeriya na kulle a gidan Kaso na Kasar.
Ghana Kasa ce da take aminiyar Najeriya tun fil-azal kuma Najeriya ta rungume kasar a matsayin yaruwarta amma kuma Ghana bata ga haka ba yanzu, tana yi wa kasar da ‘yan Najeriya cin mutunci da ba a taɓa tsammani ba.
A dalilin haka ba za mu yadda da haka daga yanzu ba. Ƙasar Ghana ta shiga taitayinta tunda wuri.” Inji Lai Mohammed.
Discussion about this post