Muzguna wa ƴan Najeriya: Ghana ta ƙaryata zargin gwamnatin Najeriya

0

Ministan Ƴada labarai na kasar Ghana Kojo Nkrumah ya karyata korafin da ministan Ƴada labarai na Najeriya, Lai Mohammed na zaegin gwamnatin kasar da muzguna wa Najeriya.

Idan ba a manta ba minista Lai Mohammed ya zargi kasar Ghana da muzguna wa ƴan Najeriya dake zaune a kasar da kuma tsananta musu a harkokin su na sana’a a kasar.

Sannan kuma ya kara da cewa baya ga wannan matsi gwamnatin kasar da gangar ta rushe wani gini mallakin Najeriya kuma ta kwace wani ginin da gangar wanda shima mallakin gwamnatin Najeriya ne.

Sai dai kuma mahukunta a kasar Ghana sun karyata wadannan zargi masu yawa.

Da farko dai ya ce gine-ginen da Lai yake magana akai, duk wa’adin da aka ba Najeriya na mallakar su duk sun cika shekaru da dama da suka wuce, kuma Najeriya bata zo ta sabunta damar cigaba da mallakar wadannan gine-gine.

” Sannan kuma ba gaskiya bane wai muna dawo da ƴan Najeriya haka kawa tare da yi musu tsanani a wajen yanke musu hukunci. Wadanda muka dawo da su duk masu laifi ne. Daga wadanda suke sana’ar Karuwanci ne, sai masu safara da ta’ammali da muggan kwayoyi, sai kuma wadanda basu da takardu na izinin zama a kasar.

” Maganar Shaguna da sabunta takardun zama a kasar kuwa, ba ƴan Najeriya bane kawai dokar ta shafa. Sabbin dokokin kasar ne kuma har da wasu ƴan kasar dake Ghana ta shafa.

A karshe Nkurma ya bayyana cewa shugaban kasar Ghana da na Najeriya za su gana nan ba da dadewa ba domin a samu natsuwa a tsakanin juna kamar yadda ya kamata kuma ake a da.

Share.

game da Author