Mun kakkabe Boko Haram daga Arewa maso Gabas, saura burbushin wadanda ke Barno kadai -Buratai

0

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa a yanzu an fatattaki duk wasu ‘yan Boko Haram daga yankunan Arewa maso Gabas, babu saura sai burbushin wadanda ke cikin Jihar Barno kadai.

Buratai, wanda ya na daya daga cikin manyan hafsoshin Najeriya da dimbin jama’a ke ta kiraye kirayen a tsige saboda tabarbarewar matsalar tsaro, ya ce sojoji na musayar bayanan sirrin yadda za a ga bayan ‘yan ta’adda baki daya daga Jihar Barno.

“Babu sauran ‘yan Boko Haram a jihohin da ke makwautaka da Barno. Saura burbushin da suka rage a cikin Jihar Barno kadai. An fatattake su, saura na boye a wani lungun cikin Barno.”

Haka Buratai ya bayyana a cikin sanarwar da kakakin yada labarai na Shugaba Muhammdu Buhari, mai suna Garba Shehu.

“Mu na samun hadin kai da jama’a da sarakunan gargajiya, kuma mu na kokarin kara kaimin da muke yi. A yanzu abin da mu ke da bukata shi ne a kara hakuri. Guyawun mu ba za su yi sanyi har mu yi jan-kafa kan gagarimin aikin da ke gaban mu ba.

Yayin da Buratai ke bugun kirji a gaban Buhari cewa babu Boko Haram a sauran jihohi banda Barno, cikin watan Mayu, Boko Haram sun kai hari a Dapchi cikin Jihar Yobe. Kafin nan a cikin Fabrairu sun kai hari a kauyen Babban Gida duk a cikin Jihar Yobe.

A nasa bangaren, Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa geamnonin yankin Arewa maso Gabas cewa har yanzu Najeriya ba ta kauce ko karkace daga bin turbar tabbatar da tsaron kasar nan ba.

Buhari ya ce Najeriya na kara bijiro da sabbin dabarun yaki da kuma makamai na zamani domin yi wa Boko Haram kwaf-daya.

“Za a samar da cikakken tsaro a Barno da Najeriya baki daya.” Inji Buhari.

“Ina tabbatar muku ku gwamnonin yankin Arewa maso Gabas cewa da tunanin yadda za a samar da cikakken tsaro a yankunan mu ke barci, kuma da su muke tashi. Duk gwamnatin da ta san abin da ta ke yi, ta san wannan nauyi ne da ya wajaba ta sauke wa al’ummar.”

Buhari ya ce fantsamar cutar Coronavirus a duniya ya kawo tsaikon wadatar wa sojoji da makamai da kuma kayan gyara.

Wadanda suka halarci taron baya ga gwamnonin akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Babban Hafsan Tsaro, sauran Manyan Hafsoshi, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da kuma shugabannin fannonin Hukumomin leken asiri.

Share.

game da Author