Mummunan rikici ka iya hargitsa zaben Edo, idan Buhari bai dauki kwakkwaran mataki ba -Kungiyar AI

0

Kungiyar Afuwa ta Duniya (Amnesty International), wadda ke gudanar da ayyukan jinkai kan ‘yancin dan adam, ta nuna matukar damuwa da yadda ake ta rura wutar siyasa gabatowar zaben gwamnan jihar Edo da za a yi a ranar 19 Ga Satumba, 2020.

Cikin wani jawabi da kungiyar ta turo wa PREMIUM TIMES a ranar Laraba, ta ja hankalin Shugaba Muhammdu Buhari da gwamnatin sa su maida himma wajen kauce wa mummunan tashin hankali a lokacin zaben.

Ana ci gaba da samun rahotannin tashe-tashen hankula, kalaman kiyayya da yi wa rayukan jama’a barazana tun ma kafin zuwan ranar zaben wanda za a gudanar cikin watan Satumba.

Za a fafata zaben ne tsakanin dan takarar APC, kuma wanda gwamnatin Buhari ke goyon baya, Ize Iyamu. Zai fafata shi da Gwamna Obaseki, wanda ya yi tsallen-gada daga APC ya koma PDP.

Daraktan Tsaro na Kungiyar Afuwa ta Duniya, Osai Ojigho, ya yi tsinkayen sakacin gwamnatin tarayya da kuma ko in kula da tsarin shari’ar kasar nan ke yi wa fitinannun da ke ruruta wutar rikicin siyasa a wannan mawuyacin yanayi a Jihar Edo, na nuni da cewa akwai yiwuwar barkewar mummunan rikici a ranar zabe da kuma bayan zaben.

“Yadda bangarorin adawar siyasar biyu ke kartar kasa su na cika-baki a kan zaben Edo, ya isa gwamnati ta lura da cewa akwai bukatar daukar kwakkwaran mataki domin hana barkewar tarzoma a ranar zabe da bayan zabe.”

Ojigho ya yi kira ga Gwamnatin Buhari ta hukunta duk wani babban dan siyasar da ya yi amfani da ‘yan ta-kife ya hargitsa zabe.

Ya kuma ce gwamnati ta tabbatar ba a tauye wa ‘yan jarida da kungiyoyin sa-ido hakkin su na lura da yadda zabe ke tafiya ba.

Share.

game da Author