MATSALAR TSARO: Yadda Arewa ta kamo hanyar durkushewa

0

Yayin da Arewa ke faman da-na-sanin haihuwar wasu bijirarrun ‘ya’yan ta da ke neman kashe uwar ta su da sauran milyoyin ‘yan da uwar ta durkusa ta haifa, PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin yadda wadannan ‘ya’ya suka yi nisa, ba su jin kira. Kuma da alama babu wani mai karfi ko gangamin taron-dangin da zai iya hana su yi wa sauran dangin na su kisan-kare-dangi. Za a fahimci shin wadannan fandararrun ‘ya’ysn Arewa, shin bakin-uwa ne ya bi su ko kuwa sakacin iyaye ne? Ko kuwa ‘ya’yan ‘shegu’ ne ke neman fasa Arewa da rana tsaka?

‘Yan ta’adda, ‘Yan Boko Haram, ‘Yan bindiga, ‘Yan samame, ‘Yan takife, ‘Yan garkuwa da mutane. Dukkan wadannan ‘ya’ya da Arewa ta haifa a yanzu, ta taba haihuwar masu irin mummunar dabi’ar su ta tayar da zaune tsaye su na kai hare-haren yaki da kamen bayi da samame da banka wa kauyuka wuta da satar dukiyoyi.

Sai dai kuma mutanen yanzu ba su san wadancan ‘ya’yan ba, sai labarin su suka rika ji ko karantawa a littattafan tarihi.

Shekaru sama da 100 bayan murnar ganin Arewa ta yi sam-barkar rabuwa da fitintinun kangararrun ‘ya’yan ta. Sai kuma ga shi daga shekaru 10 zuwa yau, Arewa ta haifi mugayen irin da ke neman su ruguza ta baki daya.

Babu wani labarin da ake kwana ana tashi da shi sai labarin kisa, kisa, kashe-kashe, hare-hare, garkuwa da mutane da sauran nau’ukan ta’addancin da ke hana zaman lafiya a Arewa.

Tun ana lissafin yawan wadanda ake kashewa a kullum, har an gaji an daina. Tun ana zaman jimami, har kisan na neman zama jiki, yadda yawan jinainan da ake zubarwa bai hana gudanar da shagulgula ba a Arewa.

‘Yan Arewa da a can baya ba su san ma’anar ‘yan gudun hijira ba, a yau an wayi gari a Arewa mafi dandazon ‘yan gudun hijira suke a Afrika. Ko a duniya ma ana buga misali da yawan dandazon ‘yan Arewa da ke gudun hijira a sansanonin cikin kasar da kuma kasashe makauta.

A kullum dan Arewa kan ambaci kalmar ‘lafiya’ sau da dama. Da ya tashi da safe zai yi gaisuwar ‘ka tashi lafiya?’ Amma a yau kowa a Arewa ya san babu lafiya a yankin, kuma babu zaman lafiya. Ba a kwana lafiya ba, ballantana har a zauna lafiya.

Kashe-kashe a Barno. Kashe-kashe a Yobe. Hare-hare a Adamawa. Tashe-tashen hankula a Taraba da Benuwai da Filato. Hare-hare a Nasarawa da Kogi da Kaduna, tsohuwar hedikwatar Arewa wadda a yanzu ta zama sarka-uwar-rikicin zubar da jinainai.

Jihar Zamfara wadda kadan ya rage ta tashi daga jiha a Najeriya ta koma ‘daular ‘yan bindiga’. Sakkwato na kan dandana kudar haihuwar mugayen irin ‘ya’yan da Arewa ta haifa, suka zame mata ‘ya’yan Allah-wadai.

Ita kuwa Jihar Katsina, za a iya cewa ta ga samu kuma ta ga rashi. Yayin da dan ta Muhammdu Buhari ya zama Shugaban Kasa tun a 2015. Maimakon su gani a tunda su ke da wuka da naman Najeriya a hannun su, sai ya kasance gagarimar matsalar tsaro ta buwayi jihar, Katsina har yanzu ta ke fuskantar tashin hankalin da rabon da haka ta faru tun lokacin yake-yaken ‘katilan-makatulan.’

Buhari: Tsakanin yaki da ta’addanci ta yafe ya ‘Yan ta’adda kisan dimbin Jama’ar da suka yi:

Babban dalilin zaben Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 da 2019 ba su wuce kashe cin hanci da rashawa ba da kuma magance matsalar tsaro, musamman ta Boko Haram a Arewa.

Sai dai kuma yayin da Buhari bai gama rabuwa da ‘Bukar’ ba, sai Arewa ta haifar wa ‘Bukar’ kani mai suna ‘Habu’. Wato ga bala’in Boko Haram ga kuma na ‘yan bindiga.

‘Yan bindiga na ci gaba da bindigewa da sace al’ummar kananan hukumomi da dama a Katsina, jihar da Shugaba Buhari ya fito.

Kananan Hukumomi irin su Batsari, Jibiya, Danmusa, Dutsinma, Kurfi, Safana, Sabuwa, Dandume, Faskari da sauran su, duk babu zaman lafiya saboda yadda ‘yan bindiga ke bin jama’a har gida suna yi musu tsintar-farin-balbela.

Allah kadai ya san yawan mutanen da Boko Haram suka kashe a Arewa. Allah kadai ya san yawan bama-baman da Boko Haram suka tada a Arewa. Allah kadai ya san yawan garuruwa da kauyukan da Boko Haram suka tarwatsa ko banka wa wuta a Arewa. Allah kadai ya san yawan jami’an tsaron da Boko Haram suka kashe a Arewa. Allah kadai ya san yawan marayun da suka rasa iyaye sanadiyyar hare-haren Boko Haram a Arewa. Kuma Allah kadai ya san yawan mutanen da Boko Haram suka nakasa a Arewa. Sannan kuma Allah kadai ya san yawan bilyoyin dalolin da aka kashe a kan yaki da Boko Haram a Arewa.

Tun ana cewa an kusa kakkabe su, har aka dawo ana cewa an kakkabe su, sun gudu sun bar takalman su. Yanzu kuma aka dawo ana kama su, ana yafe musu bsyan an yi musu “wankin kwakwalwar kankare musu mummunar dabi’ar ta’addanci a zukata’ Har yanzu ‘yan Arewa sun kasa gane fa’ida ko alherin da ke ciki.

Cukuikuyayyen Kullin Da Ya Harde Yakin Boko Haram:

Idan mai karatu na so ya fahimci halin da ake ciki a kan Boko Haram a Arewa, to ya karanta wani rubutu da Mashawarcin Gwamnan Barno Kan Harkokin Yada Labarai, Isa Gusau ya yi a ranar Litinin din nan, 10 Ga Agusta, 2920.

Rubutun na sa mai fassara kamar haka:

BORNO: Idan Ka Samu Kan Ka A Halin Da Zulum Ya Ke, Ya Za Ka Yi?”, an buga shi a jaridu kuma Isa Gusau ya watsa shi a shafin sa na Facebook.

Ga tsakuren wani sashi na rubutun na sa a kasa domin mai karatu ya wanke idon sa garau:

Boko Haram: Yadda Zulum Ya Gana Da Buhari Sau 5, Ya Kebe Da Buratai Sau 20 Cikin Watanni 15:” Isa Gusau

“A ranar 39 Ga Mayu, 2019, kwana daya bayan rantsar da Zulum Gwamnan Jihar Borno, farkon abin da ya fara yi shi ne taron sirri da manyan kwamandojin sojojin da ke yaki da Boko Haram. Daga nan kuma sai ya kira taron tattauna matsalar tsaro da sarakunan gargajiya.

“A ranar 7 Ga Yuni, 2019, Zulum ya halarci gagarimin taro kan matsalar tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar sa, cikin Villa. Shi ne taron farko da Zulum ya fara halarta, kuma matsalar Boko Haram ce babbar ajandar wannan ganawa ta sirri da aka yi.

“Ranar Laraba, 19 Ga Yuni, 2019, Zulum ya nemi alfarmar ganawar sirri shi da Shugaba Buhari, su biyu kadai, inda a wannan ganawar ce ya baje wa Buhari matsalar sake fantsamar hare-haren Boko Haram a Borno.

“Ranar Juma’a, 23 Ga Agusta, 2019, bayan Boko Haram sun kai hare-hare a Gubio, Magumeri da Konduga, Zulum ya sake komawa Fadar Shugaban Kasa, inda ya kara yin ganawar sirri su biyu, shi da Shugaba Buhari.

“A wurin wannan taro, Zulum ya nuna wa Buhari cewa bai gamsu da yadda ake tattara sojoji jingim a ‘sansanonin musamman’ ba, maimakon a rika bin irin salon yakin da aka rika yi cikin 2016 aka samu gagarimar nasara. Kwana daya kafin wannan rana, wato Alhamis, 22 Ga Agusta, sai da Zulum ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, duk dai a kan wannan matsala.

“Ranar Laraba, 12 Ga Fabrairu, 2020, Zulum ya yi ganawar sirri da Shugaba Buhari a Maiduguri, lokacin da Buhari ya je ta’aziyya, jaje da alhinin kisan matafiya 30 da Boko Haram suka yi a Auno.

“Ranar Alhamis, 9 Ga Afrilu, 2020, Zulum ya sake komawa fadar Shugaban Kasa domin sake yin wata ganawar sirri da Shugaba Buhari, domin tattauna abin da zai iya biyo bayan fatattakar da Shugaban Chadi da kan sa ya yi Boko Haram. Zulum ya nuna damuwa cewa ‘yan ta’adda daga cikin Chadi su na kwararowa cikin Najeriya, ta bangaren Tabkin Chadi.

“Ranar Litinin, 15 Ga Yuni, 2020 (kwana biyar tsakani kenan), Zulum ya sake komawa fadar shugaban kasa ya sake yin ganawar sirri su biyu, shi da Shugaba Buhari. A lokacin ne Boko Haram suka kai mummunan harin da suka kashe sama da mutum 80 a wani kauyen cikin Karamar Hukumar Gubio.

“A cikin watanni 15, Gwamna Zulum ya yi ganawar sirri da Shugaba Buhari sau biyar, kuma ya gana da Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai har sau 20, baya ga yawan kiran sa a waya da ya ke yi.

“Bayan haka, Zulum ya sha yin tarukan sirri kan matsalar tsaro da sauran Manyan Hafsoshin Najeriya da kuma Ministan Tsaro.

“Zulum ya sha yin ganawar sirri da fiye da sau 100 shi da kwamandojin yakin da ‘yan Boko Haram, Manyan Kwamandojin Kasa, Kwamandojin Birged-Birged da manyan jami’an tafiyar da yakin ‘Operation Lafiya Dole’, Rundunar Sojan Najeriya ta 7 da kuma birged-birged din da ke fadin jihar Borno.

“Cikin Janairu, 2020 Zulum ya kai ziyara N’jamena, babban birnin Chadi, inda ya gana da manyan kwamandojin da ke hedikwatar Sojojin-Kasashen-Taron-Dangi.

“Kai, Zulum har rana daya ya ware domin yin azumi da addu’o’in neman Allah ya tabbatar da nasarar shirin wanzar da zaman lafiya da lumana wanda sojoji suke ta kokarin aiwatarwa. A ranar Litinin 24 Ga Fabrairu, Musulmi da Kiristocin Borno da wasu wurare duk suka amsa kiran Zulum, suka tashi da azumi.

“Cikin watanni 15 Zulum ya amince ya samar wa sojoji Toyota Hilux guda 400 domin yaki da Boko Haram. Kuma Gwamnatin Jihar Barno na tainaka wa wadannan motoci da mai da dawainiyar gyara.

“Zulum ya na talafawa iyalan sojoji, musamman wadanda suka rasa rayukan su a wurin gumurzun yaki. Kuma Zulum kan je har a sansanonin sojoji domin kai musu ziyarar Kara musu kwarin guiwa a sansanoni daban-daban da ke cikin kananan hukumomi 27 a Borno.

“A Gidan Gwamnati kuwa, Zulum na yi kwamandojin sojoji kyakkyawar tarba, ko su ko ma duk wasu shugabanin bangarorin tsaro. Ki an san da zuwan su ko ba a sani ba, duk wanda ya je gidan gwamnati zai shiga Ofishin Zulum su gana duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

“Kai, irin wannan goyon baya da Zulum ke bai wa sojoji ya sa a ranar 24 Ga Mayu, 2020, Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana a bainar jama’a cewa, goyon bayan da Zulum ke bai wa sojoji ba zai iya “misaltuwa ko kwatance ba.”

“Ko kafin jinjinar da Buratai ya yi wa Zulum, Ministan Tsaro Manjo Janar (mai ritaya) Bashir Magashi ne ya fara yi masa jinjina a raanrt 16 Ga Disamba, 2019. Magashi cewa ya yi, “Zulum Gwamna ne da ya sadaukar da kan sa da lokutan sa kacokan wajen bunkasa shirin yaki da Boko Haram.”

Ba Sojoji Kadai Zulum ya ke Tallafawa ba

“Tun a makon farkon da aka rantsar da shi Zulum ya kara wa dubban dakarun CJTF da maharba da ‘yan bijilante kudaden alawus din su. Kuma ya kara musu kayan aiki saboda ya san irin gudummawar da suke bai wa sojoji.

“Zulum ya kafa Gidauniyar Tallafawa Ga Harkokin Tsaro, ya karbi bakuncin taron jihohin Arewa maso Gabas a kan Matsalar Tsaro. Ya na halartar duk wani taron tattauna matsalar tsaron da aka gayyace shi, a Borno ko a wajen jihar.

“Sai dai kuma duk da irin wannan yunkuri da kokari da jajircewa, ana ci gaba da karkashe daruruwan mutane a Borno. Bayan wadannan kashe-kashe da Boko Haram ke yi, su na fatattakar jama’a daga gidajen su.

Su Wa Suka Bude Wa Zulum Wuta A Baga?

“An kai wa Gwamna hari a Baga, inda kwamandojin sojoji suka shaida wa gwamnan cewa babu Boko Haram a yankin.

“Shin idan haka ne, wa ya kai wa Gwamna Zulum hari kenan? ‘Yan Boko Haram din da babu ko daya ne suka Kai masa hari, ko kuwa fatalwar su ce?

“Ga shi kuma ba a daina kama jama’a ana arcewa da su ba, ana nuno bidiyon yi wa mutane kisan-gilla.

“Yanzu don Allah wane shugaba ne zai iya jure wannan abin takaici ya yi shiru saboda gudun afkawa tarkon siyasa? Idan ya yi shiru bai yi magana ba, to wa zai yi magana a madadin wadanda aka kassara da wadanda aka fatattaka daga gidajen su?

“Shin wace murya ce ta fi ta gwamna karfi da har za ta fi ta sa yin kururuwar neman agaji a saurare ta fiye da ta Gwamna Zulum?

“A takaice, idan ka samu kan ka a irin halin da Zulum ke ciki, me za ka yi ne kai?” Karshen bayanin Kakakin Gwamna Zulum kenan.

Amma kuma duk a cikin wannan kwatagwangwamar ce Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya ce an fatattaki Boko Haram a sauran jihohi, sai burbushin wadanda suka rage a Barno kadai.

Share.

game da Author