MATSALAR TSARO: Abin da ya sa na caccaki Sojojin Najeriya – Zulum

0

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, ya ce ya soki lamirin Sojojin Najeriya ne domin ya ga cewa sun kara himma da gwazo, amma ba raina kokarin su ya yi ba.

Zulum ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke bude Cibiyar Horas da Dabarun Yaki da Zaman Lafiya da aka gina a garin Buratai, cikin Karamar Hukumar Biu, Jihar Barno.

Buratai can ne kauye mahaifar Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, cibiyar dai wani bangare ne na Jami’ar Sojoji da aka gina a Biu. An kuma sa wa cibiyar suna Tukur Buratai.

Kwanan baya Zulum ya rika surfa wa sojoji bakaken kalamai masu kaushi da zafi sosai, har ya rika zargin su da cewa rashin katabus din su ne ya sa Boko Haram suka juya kan jama’a su na kai manya da kananan hare-hare.

Cikin watan Fabrairu, Zulum ya zargi sakacin sojoji ne ya haddasa kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya 30 da suka yi kwanan-hanya kafin su shiga Maiduguri.

Kwanan nan kuma ya zargi sojoji da hannu wajen kai wa tawagar sa har da shi kan sa hari a garin Baga,cikin Karamar Hukumar Kukawa.

Kwanan nan kuma ya zargi sojoji wajen kai masa mummunan farmaki da aka yi, inda ya ce sojoji ne suka kai masa Hari a wani rangadi da ya fita a Monguno da Baga, domin ya raba kayan tallafi a Sansanonin Masu Gudun Hijira.

Amma da ya ke magana wajen bude cibiyar, Zulum ya gode wa Sojojin Najeriya, bisa kokarin da su ke yi da jajircewa kan yaki da ta’addanci.

Zulum ya ce cibiyar za ta bada kofa wajen nazarin lalubo mafitar matsalolin tsaro daban-daban.

Buratai ya bada umarnin gyara Cibiyar Kula da Lafiya ta garin Buratai da kuma gina wata babbar makaranta a garin.

Share.

game da Author