Babu irin matakai da zaman shawarwarin da ba a yi wajen neman mafitar shawo kan matsalolin tsaro a Arewa. Amma har yau abu ya gagara.
Babban abin haushi da takaici bai wuce a ce halin ciwo daban, magani kuma daban da ake yi wa lamarin ba.
Farfaganda da taron kashe tsawon lokaci ana Turancin kokarin kawo karshen lamarin ya yi yawa matuka. Domin ba a cika sanya talakawan da rikicin ya fi shafa ba wajen neman magance lamarin.
Misali, Shugaba Muhammadu Buhari ya Kai ziyarar jaje a farkon shekarar nan a Batsari, Jihar Katsina. Maimakon a bari ya ji ta bakin al’ummar garin, sai aka hana kowa yin jawabi, har da Hakimin Batsari.
Tunda Mai daki shi ya san inda dakin sa ke zuba, to shi ne ya fi dacewa ya nuna wa mai gyaran daki inda ruwa ke yoyo?
Akasarin talakawa da duk wani da ba ya iya magance wa kan sa wannan rikice-rikice idan sun tunkaro shi, da kuma wadanda ba su da jami’an tsaron da ke kare lafiyar su, na mamakin wadannan bayanai da ke kasa:
Mamakin Sojoji: Jama’a na mamakin cewa matsawar Boko Haram za su rika kai wa sojoji fsrmaki, washegari sojoji su bada sanarwar cewa sun kori ‘yan ta’adda sun gudu, to babu ranar daina yaki da Boko Haram.
Tambayar da ke fitowa daga bakin jama’a ita ce, shin me ya sa idan sun gudu ba za a bi su har mabuyar su ba?
Mamaki kan ‘Yan Sanda:
Ta yaya barayin shanu za su shiga kauye ko rugar Fulani su kora shanu 100 har zuwa 200, amma a kasa bin sawun su har a ga inda suka yada zango ko suka boye?
Ta yaya za a shiga rugar Fulani a kashe shanu birjik sama da 30, a kwashe kamar 50 amma a ce ba ku san inda aka nufa da su ba?
Ta yaya ku ke tsammanin za ku kama barayin shanu ku kai su kotu, amma bayan sati daya ko biyu su shigo garin da suka yi satar su ci kasuwa su koma yankin su? An so zaman lafiya kuwa?
Ta yaya kabilun da ba su da ko akuya za su yi rikici da Fulani, su kwashi shanun su, har su rika yankawa su na watanda, sannan a ce ana so a zauna lafiya?
Ta yaya Bafulatanin da ke tsoron babur, amma aka wayi gari shi ke tare mota da bindiga ya yi gaba da fasinjoji ya yi garkuwa da su?
Me ya sa aka fi gano mabuyar ‘yan bindigar da suka saci wani babba, ta hanyar gano lambar waya. Amma idan tantirin talaka aka yi garkuwa da shi, gsnowa ta lambar waya ba a yin nasara?
Mamaki kan Gwamnati:
Ana mamakin yadda gwamnatin jihohi ke shirya taron sasantawa da barayi, amma ta ke mantawa da batun duba yiwuwar biyan biyyar wadanda barayin suka yi wa barna har suka raba su da garuruwan su.
Ana mamakin yadda gwamnati ta yi duk wani abin da za ta iya har ta hana shigo da shinkafa da wasu kayayyakin masarufin da talaka ke amfani da shi. Amma kuma a kasa gane yadda ake shigo da manyan bindigogi a Arewa, kai ka ce babu jami’an tsaro a kan iyakokin shigowa Najeriya daga waje.
Gwamnati ta kasa hana matsalar kwararowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar ko wasu kasashen da ke makwautaka da Najeriya.
Ya aka yi gwamnonin Arewa suka ki maida hankali wajen kafa dokar takaita wa masu kiwo kaura daga wannan wuri zuwa wancan?
‘Mahaukata’ Biyu Masu Wahalar A Yi Musu Magani:
Mahaukaci na farko shi ne Bafulatanin da zai iske amfanin gona, amma ya bar shanun sa su shiga cikin gona su yi mummunar barnar cinye amfanin gonar.
Mahaukaci na biyu, shi ne mai gonar da aka ci wa amfanin gona na naira N3, 500 amma sai ya fusata ya kashe saniya kamar goma.
Bafulatanin da ya fi shi hauka kuma shi ne wanda zai kashe mai gona da ‘ya’yan sa hudu.
Shin jama’a ina mafiya?