Ranar Juma’a ce Majalisar Dattawa ta rubuta wa Hukumar Hukumar Hada-hadar Cinikin Mai ta Kasa (DPR) kakkausar wasikar neman sanin yadda aka yi da cinikin fetur na naira tiriliyan 2.4 a cikin 2019.
Majalisa ta nuna damuwa ne ganin yadda alkaluma suka nuna cewa naira bilyan 44.5 kadai DPR ta saka a cikin Asusun Ajiyar Cinikin Fetur (CRF), maimakon naira tiriliyan 2.4 a shekarar 2019.
Majalisa ta nemi sanin yadda aka yi da kudaden da kuma dalilin da ya sa ba a zuba su a asusun da doka ta ce a rika zuba su ba.
Hakan kuwa ya taso ne bayan da shugabannin hukumomin tara kudaden shiga daban-daban suka ki bayyana a gaban Kwamitin Majalisa Mai Lura da Kasafin Kudi da Tsare-tsare, domin su yi bayanin kintacen kudaden shigar da suka ce za su samu a cikin kasafin 2021.
Shugaban wannan kwamiti, Solomon Adeola ne ya fara tayar da wannan balli, a lokacin da ya nemi sanin adadin kudaden shigar da Hukumar DPR ta tara a shekarar 2019.
“Saboda mu dai rekod din kudade da bayanan da ke a gaban mu, wadanda daraktocin hukumomi suka gabatar, babu takamaimen cikakken bayanin kudaden da DPR ts zuba a Asusun Cinikin Fetur na shekaru uku, kuma babu kintacen kudaden shigar da DPR ke ganin za ta iya samu a cikin kasafin 2021.
“Idan har ana so wannan kwamiti ya yi aikin da ya dace kamar yadda ka’ida da doka suka tanadar, to tilas sai an gabatar mana da cikakken bayanin yadda aka gudanar da tasarifin wadannan makudan kudade. Mu na so a kawo mana a ranar Litinin, sannan kuma Daraktan DPR da sauran manyan jami’an hukumar su bayyana a gaban wannan kwamiti a ranar Talata.
“Sannan kuma tilas a hado da cikakken bayanin kintacen kudaden shigar da ake sa ran samu a cikin kasafin 2021-2022.” Inji Adeola.
Kafin a zo nan kuwa, Shugaban Bangaren Tsare-tsare na Hukumar DPR, Johnson Ajewale, wanda ya yi wa ‘yan kwamitin majalisa jawabi saboda Babban Daraktan DPR, Sarki Auwalu bai halarci taron ganawa da kwamitin majalisa ba, ya ce DPR ta yi cinikin fetur din naira tiriliyan 2.4 a 2019, amma naira bilyan 44.5 kadai ta zuba a cikin Asusun Cinikin Fetur.
Duk wani kokarin da Shugaban Bangaren Kudade na DPR, Lilian Ufondu ta yi domin ta fayyace musu wannan wawakeken gibin makudan kudade na fitar-hankali da aka yi, duk ba ta gamsar da ‘yan kwamitin ba, sai ma kara harzuka su da ta yi.
‘Kame-kamen Yadda Aka Yi Da Naira Tiriliyan 2.4’:
Lilian ta ce a cikin wadannan makudan kudade an cire naira bilyan 88, kudin ladar karbar kudaden cinikin mai, wato kashi 4% bisa 100%.
Daga nan sun ci gaba da zabga mata bulalar ruwan tambayoyin yadda aka yi da sauran kudi sama da naira tiriliyan 2. Amma daga ta ce an gudanar da ayyukan yau-da-kullum da su, sai ta ce an aiwatar da ayyukan kacaniyar gudanarwa da su, ba tare da gabatar da alkaluman adadin ko nawa aka kashe dalla-dalla a fayyace ba.