Mahara dauke da bindigogi sun kashe dan majalisar dokokin dake wakiltar Baraza/Dass a majalisar Bauchi, Musa Mante, sannan sun arce da iyalan sa.
Wata majiya ta tabbatar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Bauchi ranar Juma’a.
Majiyar ta bayyana cewa maharan sun kashe Mante a gidansa a daren Alhamis.
Sai dai kuma ana ta rade-radin cewa maharan sun dira gigan Marte don su yi masa fashi ne.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar’Yan sanda Ahmed Wakil ya tabbatar da aukuwar haka yana mai cewa maharan sun yi garkuwa da matan Mante guda biyu da dansa daya.
Wakil ya ce rundunar za ta sanar wa manema labarai da zaran sun sami cikakken bayani game da abin da ya faru a gidan Mante.
Discussion about this post