Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da mutuwar wani bature da mahara suka yi garkuwa da shi da wani dan Najeriya tsakanin kauyukan Yankila da Regina a karamar hukumar Rafi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Usman ya bayyana cewa jami’an tsaro sun tsinci gawar baturen a dajin Pangu Gari dake karamar hukumar Rafi.
Ya ce an Kai gawar babban asibitin Minna domin gudanar da bincike a kai.
Usman ya ce yanzu dai jami’an tsaro na gudanar da bincike domin ceto dan Najeriyan dake hannun masu garkuwa da mutane.
Ya yi kira ga mutane musamman wadanda ke da bayanan da za su taimaka wajen kamo masu wadanda suka yi garkuwa da su.
Idan ba a manta ba rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana garkuwa da akyi da wadannan mutane.
Kwamishinan ‘yan sanda Adamu Usman ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Minna ranar Talata.
Adamu ya ce dan kasar wajen da dan Najeriyan na aiki da Kamfanin ‘Transparent construction’ dake gyaran babban titi a yankin.
An yi garkuwa da wadannan mutane ranar 17 ga watan Agusta da karfe 11:05 na dare.
Ya ce rundunar bata da masaniyar aiyukkan da Kamfanin ke yi a yanki amma an aika da jami’an ta domin ceto da kamo wadanda suka yi garkuwa da mutanen.
An tabbatar cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da su a wurin aikin wata rijiyar danyen man fetur a Abua, dake jihar.
Gamayyar jami’an tsaro na JTF da aka tura yankin Neja-Delta domin kula da tsaron rijiyoyin mai sun tabbatar da sace Turawan su biyu.
Discussion about this post