A yayin da ƙasashen Turai ke cigaba da yin gwaje-gwaje ingancin maganin Korona da suka hada, Najeriya ma ba a barta a baya ba wajen hadawa da yin nata gwajin magungunan.
Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa tana yun gwajin magungunan warkar da Korona har guda 40 da masu hada magungunan gargajiya suna mika wa hukumar.
Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta sanar da haka ranar Talata a garin Abuja.
Mojisola ta ce ana yin gwajin ingancin magungunan ne saboda kada wajen neman kiba a samo rama.
“Tun bayan bayyanar annobar Korona, masu hada maganin gargajiya suka fantsama bincike domin ganin suma ba a barsu a baya ba wajen ganin an hada maganin cutar. Da yawa cikin su sun mika samfarin maganin su ga hukuma domin yin gwaji da tantance ingancin sa.
” Haka kuma NAFDAC ta gindaya musu wasu sharudda da dokoki da za su bi wajen hada maganin.
“Za a yi gwajin ingancin magungunan a dabbobi a karon farko tukunna.
Mojisola ta gargadi masu maganin kada su kuskura su jaraba wani magani ba tare da hukumar ta bada daman haka ba.
A watan Mayu ne hukumar NAFDAC ya bayyana cewa a soshiyal midiya da shafukan jaridu ne kadai ake ganin labarai na masu ikirarin cewa sun gano maganin gargajiya wanda zai warkar da cutar Coronavirus.
Adeyeye ta bayyana cewa har mutum daya ne tak ya tunkari hukumar NAFDAC ya nemi ta duba ingancin maganin da ya yi ikirarin cewa ya hada na gargajiya, da ya ce zai iya warkar da Coronavirus.
“Shi ma wancan mutum dayan, ba wai maganin cutar ce gidigat ya ce ya gano ba. Cewa ya yi ya gano maganin alamomin rashin lafiyar da ake ganin su ne alamomin kamuwa da cutar.
Sai dai kuma tun bayan haka wasu masu maganin suka rika tunkarar hukumar da nasu hadin.