Maganin Korona da Rasha ta hada zai yi aiki a jikin masu shekaru 18 zuwa 60 ne – Inji Bondarev

0

Babban Jami’i a sashen masana kimiyyar magunguna na ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Rasha Vladimir Bondarev ya bayyana cewa maganin rigakafin Korona da kasar Rasha ta hada zai fi tasiri ne akan wadanda shekarun su bai wuce daga 18 – 60 ba.

Bondarev ya fadi haka a taron manema labarai da aka yi a Moscow, babban birnin kasar Rasha ranar Laraba.

Ya ce masana kimiyya za su cigaba da gudanar da bincike domin ganin maganin ya yi wa mutanen da suka dara shekaru 60 aiki.

“Bisa ka’ida duk maganin da za a hada a kasar Rasha za a tabbatar cewa zai yi wa jarirai zuwa masu shekaru fiye da 60 aiki a jiki ba tare da sun samu matsaloli ba.

“Sai dai wannan karon masana kimiyyar magunguna da hada ta sun gwada inganci da sahihancin maganin rigakafin Korona a jikin mutane masu shekaru 18 zuwa 60 ne kuma suka gano rigakaifin zai fi yi wa wadanda ke da shekaru 18-60 ne tasiri.

Daya daga cikin masanan da suka hada maganin Alexander Gintsburg ya dara shekaru 60 kuma ya yi amfani da maganin bayan an hada.

Gintsburg ya ce tun bayan ya sha yaji jikin sa garau, babu wata matsala.

Maganin rigakafin da aka hada iri biyu ne da ake hadawa a yi wa mutum alluran su. Maganin zai karawa garmuwar jikin mitim karfi sannan ya warkar da mara lafiya.

A Yanzu dai anyi gwajin inganci da sahihancin maganin a jikin mutum 76, kuma duk sun warke ta-ta-tas garau rau.

Idan ba a manta ba a ranar Talatan wannan mako ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa masana magunguna a kasar sun kammala hada rigakafin Korona da kowa zai yi amfani da shi.

Masana kimiyar dake hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Institute’ dake Moscow ne suka hada wannan magani na rigakafi bayan akalla sun Yi watanni biyu suna gwajin inganci da sahihancin sa.

Putin ya tabbatar da inganci da sahihancin maganin yana mai cewa daya daga cikin ‘ya’yansa da ta kamu da cutar ta samu lafiya bayan ta yi amfani da rigakafin.

Ya ce yana sa ran nan ba da dadewa ba za a fara sarrafa maganin da yawa domin mutanen kasar.

Yanzu kasar Rasha ita ce kasa ta farko da ta fara hada maganin rigakafin cutar Korona da hakan zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da ake samu a kasar sanadiyyar wannan cuta.

Share.

game da Author