Idan ba a manta ba a watan Yuli ne Likitocin kungiyar NAGGMDP dake karkashin inuwar kungiyar NARD suka fara yajin aiki a dalilin rashin biyan bukatunsu da gwamnatin jihar ta ki yi.
Wadannan bukatu na kungiyar sun hada da rashin saka likitoci cikin tsarin inshoran lafiya, rashin biyan ma’aikata da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata, rashin biyan su alawus, rashin Kara wa ma’aikata girma da sauran su.
Sai dai kuma a daidai suna cikin haka a ranar Litini Gwamnatin ta biya Naira biliyan 3.13 a matsayin alawus din duk ma’aikatan lafiya dake jihar.
A dalilin haka kungiyar NAGGMDP ta janye yajin aiki da ta ke ciki a jihar wata daya da ya gabata.
Shugaban kungiyar Oluwafemi Aina ya Sanar da haka ranar Litini a garin Abeokuta.
Aina ya yi kira ga gwamnati da ta yi da gaske wajen biyan sauran bukatun ma’aikatan lafiya a jihar ke binta.
Sauran bukatun ma’aikatan lafiya da ya rage sun hada da saka duk likitoci musamman wadanda ke kula da masu fama da cutar covid-19 cikin tsarin inshoran lafiya, biyan alawus din ma’aikatan lafiya dake kula da masu fama da cutar covid-19, biyan ma’aikata da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata da dai sauran su.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 288 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –88, Kwara-33, Osun-27, FCT-25, Enugu-25, Abia-20, Kaduna-17.
Filato-13, Rivers-13 Delta-10, Gombe-8, Ogun-4, Oyo-3, Katsina-1 da Bauchi-1.
Yanzu mutum 44,129 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 20,663 sun warke, 896 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,570 ke dauke da cutar a Najeriya.
Discussion about this post