Bahaushe yace, idan sallah ta lalace, a tuhumi limami. Babu abunda ya kai kyawun zuciya mahimmanci a wajen jagoran kowacce irin tafiya. Idan akwai hali mai kyau komai zai iya samuwa.
Za a iya samun tarbiya, cigaban tattalin arziki, tsaro, farin ciki da son juna a cikin mutanen da shugabanninsu suke da kyawun hali. Adalin shugaba ba a ganeshi a fuska ko a kalamansa sai an dorashi akan mulki.
Shugaba mai kudi idan bashi da kyawun hali zai iya yin komai don ya inganta dukiyarsa kuma ya lalata dukiyar al’umma. An yi haka bila-adadin a kasar Najeriya. Ana kan yi ma. Gashi nan ana ta fama da su akan kujerar mulki. Sun rikita komai saboda biyan bukatarsu.
Hakazalika, idan shugabanku ya zama mai ilimi amma babu hali mai kyau zai kasance kamar jaki ne wanda yake dauke da littattafai. Haka nafsi yace, idan kana da ilimi baka aiki da shi baka da bambanci da jakin da aka dora masa kayan littattafai. Ilimi ba a ganinsa a cikin kwakwalwar mai shi, har sai ya aikata abunda zai bayyana iliminsa.
Shugaban da yake da zafin kai idan bashi da kyawun hali zai addabi kowa ne, har wadanda suke tare da shi zai iya shafarsu. Akwai inda zafin kai yake da amfani amma bashi da yawa sosai a cikin rayuwa.
Don da nutsuwa da hakuri ake warware matsala. Akwai wajen da zafin kai yake rikita al’amura. Ba a mulki da siffa daya. Ana amfani da sanyi da zafi ne wani lokacin.
Tabbas shugaba mai sanyi da yawa shima idan bashi da hali mai kyau hakurin nasa bashi da amfani a wajen mabiyansa saboda ba zai iya gyara abubuwa masu amfani ba idan an samu matsala. Za a iya samun wanda yana da hakuri don son zuciya da ha’inci.
Wannan hakurin bashi da amfani ga talakawa. Akwai shugaban da zai dinga yi muku fara’a amma kuma mayaudari ne, cutar daku yake yi a karkashin kasa.
Allah ya bamu shugabanni nagari.