KWARAROWAR ‘YAN AL-QIDAH: Ba gudu ba ja da baya, sojojin Najeriya na nan a shirye domin fatattakar koma waye – Enenche

0

Kodinatan yada labaran rundunar Sojin Najeriya John Enenche, ya bayyanawa ‘yan. Najeriya cewa su kwantar da hankalinsu bisa cewa da aka yi wai ‘Yan Al-Qida na nan kwararowa Najeriya.

Enenche ya ce wannan magana kamar shawara ce aka ba Najeriya da yaba yadda take ragargazar yan-ta’adda da suka kai koma a Najeriya.

” Wannan abu ba abin a tada hankali bane. Zaratan sojojin Najeriya ba a kwance suke ba. A shirye suke. Ba tun yanzu ake ba mu irin wannan shawarwari ba kuma ai kuna ganin akan kama ko kashe wadanda ba yan kasar nan bane a hare-haren ‘yan ta’adda da sojojin ke kai musu.

” A ‘yan kwanakin nan a jihar Neja dakarun mu sun damke wasu da ba ‘yan Najeriya da ke aikata ta’addanci a kasar nan. Muna nan idanuwan mu a bude kulu-kulu, ba tsoro ba ja da baya.

Enenche ya kara da cewa zuwa yanzu an samu gagarimar nasarori a wajen yaki da Boko Haram da ta’addanci a kasar nan, sauran ‘yan burbudine da ba a rasa ba. “Kuma suma mun kusa mu tarkata su.”

Idan ba a manta ba Wani Kwamanda a rundunar sojojin kasar Amurka Dagvin Anderson da ke aiki a yankin Afrika ya gargadi gwamnatin Najeriya cewa kungiyoyi irin su Al-Qida na kwararowa yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

” Yanzu haka suna samun matsuguni da gudanar da ayyukansu a yankin Arewa Maso Gabas, Musamman yankunan Barno. Yanzu kuma sun fara kafa sansanoni a yankin Arewa Maso Yamma, a Najeriya.

Jihohin Arewa Maso Yamma sun hada da, Kaduna, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina da Jigawa.

” Zamu hada kai da Najeriya domin mu rika sanar da juna bayanan sirri game da yadda wadannan kungiyoyi ke kokarin mamaye Najeriya. Kungiyoyi kamar su Al-Qida, Boko Haran, ISIS, da ISWAP. Za mu rika raba bayanan sirri a tsakanin mu domin sanin yadda za a tunkare su.

” Babu wata kasa da zata zo ta yi wa Najeriya yaki. Dole dai ita ce zata yi wa kanta abinda ya dace ko, Kasar Amurka, Britaniya, da wasu kasashe na Turai duk dai sai dai su taimaka mata amma ita ce wuka ita ce nama a wannan aiki.

” Dole sai mun fahimci mene Najeriya ke so mu taimaka mata da shi. Daganan sai gaba dayan mu mu ko mu tsara yadda za mu tsara abubuwan.

” Najeriya shirgegiyar kasa ce, daje da iyakoki da kasashe a zagaye da ita. Dole ta maida hankali wajen yin amfani da jiragen yaki na sama idan tana so da iya dakile hare-hre da kwararan ‘yan kungiyoyi haka.

Share.

game da Author