Kwamitin majalisar dattawa dake kula da harkokin Bankuna da kamfanonin Inshora karkashin shugabancin shugabancin Sanata Uba Sani ta ziyarci gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a fadar gwamnatin jihar.
Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya bayyana cewa kwamitin dungurungun sun garzayo fadar gwamnatin jihar ne domin ziyartar gwamna El-Rufai da kuma jinjina masa bisa ayyukan ci gaba da yake yi a jihar.
Kwamitin tana garin Kaduna ne domin halartar taron sanin makaman aiki da aka yi a hukumar NDIC dake Kaduna.
Bayan tattaunawa da suka yi da gwamna El-Rufai da jinjina masa bisa ayyunkan raya kasa da ya maida hankali akai a jihar Kaduna, Sanatocin sun dauki hotuna tare da gwamna El-Rufai sannan sun yi masa fatan Alkhairi a ayyukan da ya sa a gaba.
” Na yi godiya matuka bisa karrama mu da gwamna El-Rufai yayi duk da kankanin lokaci da muka sanar masa wannan ziyara na mu. Baya ga haka muna taya mutanen Kaduna murna da irin manyan ayyuka da muka ga gwamnan na yi a ko-ina a fadin jihar.” Inji Uba Sani.
A karshe sanatocin tare da Gwamna El-Rufai sun tattauna game da matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar da kasa baki daya. Sannan sun shaida masa cewa lallai suna tare dashi a kokarin sa na kawo karshe matsalar tsaro a jihar sa da kasar nan.
Discussion about this post