Kwamitin Kare ‘Yancin ‘Yan jarida ya umarci gwamnatin Najeriya ta hukunta ‘Yan sandan da suka yi wa dan jarida rubdugu

0

Kwamitin kare ‘yan jarida ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta hukunta ‘yan sandan da suka lakada wa wani dan jaridar Daily Post dukan tsiya.

Wannan dan jarida mai suna Sikiru Obarayese, ya shaida wa CPJ cewa laifinsa shine don ya dauki hoton yadda ‘yan sanda ke cin zarafin wani a lokacin da yake aikin dauko rahoto.

Wannan duka da aka yi wa Obarayese ya sa sai da aka kwantar da shi a asibiti sannan aka yi masa gwaje-gwaje.

Sai dai kuma dan jaridan ya shaida cewa akwai sauki matuka wato jikin nasa.

” Irin wannan cin zarafi da ‘yan sandan Najeriya ke yi wa ‘yan jarida a lokacin da suke aikin su nuni ne cewa lallai akwai aiki a gaba matuka game kare ‘yan cin ‘yan jarida a lokacin da suke aikin su ba a Najeriya ba har da sauran kasashen duniya.

” Dole a rika barin ‘Yan jarida na aikin su yadda ya kamata ba tare da ana muzguna musu a lokacin da suke aikin dauko labaran yadda take kayawa a kasashe game da yaki da annobar Korona.

A karshe, Obasereye ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun ya aika masa da naira 50,000 kudin maganin da ya kashe sannan ya bashi hakuri bisa abinda jami’an sa suka yi masa.

Share.

game da Author