Kungiyar Rajin Kare Muradin Harkokin Addinin Musulunci (Muslim Rights Concern, MURIC), ta yi fatali tare da kin amincewa da rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) da aka tsara lokutan su a daidai lokutan Sallar Juma’a.
An dai shirya fara rubuta jarbawar WAEC a ranar 11 Ga Agusta, amma kuma akwai lokutan da za su kasance daidai lokacin da ake jarabawar ne lokacin Sallar Juma’a.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ranar Juma’a, cikin wata wasika da Daraktan MURIC, Ishaq Akinbola ya fitar.
MURIC ta ce, “WAEC ta ki jin bari, ta sake aza lokutan rubuta jarabawar wasu darussa a daidai lokutan Sallar Juma’a, a jarabawar da za a fara ranar Talata, 11 Ga Agusta, 2020. Akwai darussan da a cikin musulmi da dama za su yi jarabawar. Wannan kuwa akwai matsala sosai kan haka.
“Mu na ganin WAEC kamar ta na kokarin kirkiro wata makarkashiyar tauye wa matasa musulmi hakkokin su da Alah Ta’ala ya ba su na gudanar da addinin su.”
Akinbola ya ce akwai makarkashiyar da wasu masu yi wa Musulunci zagon-kasa.
“Idan aka duba za a ga cewa a ranar 14 Ga Agusta, 24 Ga Agusta da 4 Ga Satumba duk ranakun Juma’a ne da aka saka lokutan rubuta jarabawa daidai lokacin da ake Sallar Juma’a.
Sanarwar ta ce da gangan aka kitsa wannan tuggu da kutunguila, ba a rashin sani ba.
MURIC ta ce sun rubuta wa WAEC wasika da suka raba wa manema labarai tun cikin watan Yuni, ta na tunatar da hukumar shirya jarabawar kada ta shirya rubuta wani ko wasu darussa a daidai lokacin tafiya Sallar Juma’a.
Shugaban na MURIC ya ce ya yi matukar mamaki ganin yadda Hukumar Shirya Jarabawar Sakandare (WASSCE) ba ta shirya jarabawa a lokutan Sallar Juma’a ba.
MURIC ta yi barazanar cewa idan Hukumar WASSCE ba ta sauya lokutan ba, to matasa musulmi za su fito su Kan titi da kansu su nuna rashin amincewa da tauye musu hakkin su da yancin gudanar da addinin su.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Ministan Ilmi su taka wa WASSCE burki daga hawan kawarar da hukumar ke wa musulmin kasar nan.
Ya ce kada Gwamnatin Tarayya ta yi mamaki idan matasa musulmi suka yi wa jarabawar tawaye, suka ki shiga, muddin ba a sauya lokutan da za a yi zarabawa daidai lokacin Sallar Juma’a ba.