Babbar Kotun Shari’a ta Yanki da ke unguwar Hausawa a Kano, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan wani matashin mawaki wanda ya yi zagi ga Manzo (SAW).
An yanke wa Yahaya Sherif mai shekara 22 hukuncin ratayewa saboda wani zagi da ya yi wa Annabi SAW kuma wanda ya janyo masa jangwangwamar da ta kai hasalallu sun banka wa gidan mahaifin sa wuta bayan fitar sakon da ya yi ta soshiyal midiya.
Waka ce ya fitar, inda a cikin ta ya aibata Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam, kuma aka watsa ta a cikin watan Maris, 2020.
Bayan an banka wa gidan mahaifin sa wuta, mahaifin ya nesanta kan sa da dan nasa kuma ya nesanta kan sa da sabon da dan ya aikata.
Ya ce babu ruwan sa da akidar dan sa, “da ina da iko, zan iya yanke masa hukunci kamar yadda musulunci ya bada umarni a yi wa wanda ya yi irin laifin da ya aikata.”
Mai Shari’a Aliyu Kani ya ce ya yi amfani da Sashe na 382 (b) na Dokar Penal Code a Kano, ta shekarar 2000.
An Yanke Wa Wanda Ya Zabga Sabo Hukuncin Daurin Shekara 10
Duk dai a rana daya, wannan kotu ta daure wani matashi hukuncin shekaru 10 a gidan kurkuku, saboda zabga sabon Allah da ya yi.
An daure Umar Farouq da ke unguwar Sharada ne bayan alkali ya jira ya kai munzilin balaga, kamar yadda Mazahabar Maliki ta tanadar.
Dukkan su dai an ba su tsawon adadin kwanaki 30 su daukaka kara.