Ministar Harkokin Agaji Da Jinkai, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa ‘yan Najeriya 198, wadanda su ka makale a kasar Lebanon sakamakon hutun dole na annobar korona, yanzu sun samu damar dawowa gida.
A cewar ministar, ma’aikatar ta, tare da hadin gwiwar Cibiyar Yaki Da Fataucin Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) da kuma Cibiyar Agajin Gaugawa ta Ƙasa (NEMA), sun tarbi wadanda su ka dawo din a ranar Laraba, 12 ga Agusta da ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2020.
A wata sanarwa ga manema labarai da aka bayar a ranar Juma’a, ministar ta kuma bayyana cewa akwai ‘yanmata ‘yan Najeriya 5,000 da su ke maƙale a Lebanon yanzu.
Ta ce, “Jimillar ‘yan Najeriya 198 wadanda su ka makale a Lebanon sun samu ‘yancin su kuma sun iso gida.
‘’Akwai akalla ‘yanmata ‘yan Najeriya 5,000 a maƙale a Lebanon bayan an ja su an kai su da sunan wai za su yi aikatau a gidaje, wanda daga cikin su Ofishin Jakadancin Nijeriya ya kammala tattara bayanai kan mutum 256 wakanda su ka amince su dawo gida.
“Ma’aikatar mu tare da cibiyoyin da abin ya shafa a arkashin ta sun sadaukar da kan su wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriyan da su ka makale a Lebanon da wasu kasashen sun dawo gida lafiya lau.”
Hajiya Sadiya ta kara da cewa gwamnati ta samu kiraye-kirayen neman agaji daga ‘yanmata ‘yan Najeriya a Saudi Arebiya, Oman, Masar da sauran sassan kasashen ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Saboda haka ta yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa, da su guji bari ana yaudarar su ta hanyar shafa masu mai a baki da alkawuran karya cewa za su samu rayuwa mafi inganci a can, nan kuwa aikin zubar da mutunci za su je yi.
Maimakon haka, ta shawarce su da su yi amfani da shirye-shirye daban-daban da ke akwai waɗanda gwamnati ta fito da su domin taimaka masu su samu hanyoyin kyautata rayuwar su a cikin Nijeriya.
Ta kara da cewa babu inda ya fi gida.
Ministar ta yaba da aikin masu ruwa da tsaki cikin lamarin irin su gwamnatin Jihar Oyo, da IOM da al’ummar ‘yan kasar Lebanon da ke Nijeriya saboda goyon bayan da su ka bayar wajen dawo da ‘yan Najeriyar gida lafiya lau.
Ta nanata cewa za a dauki bayanan dukkan wadanda su ka dawo din tare da goyon bayan hukumar NAPTIP.
Discussion about this post