Kididdigar alkaluma sun bayyana cewa cutar Coronavirus ta kashe sama da mutum 50,000 a cikin kasa da kwanaki 5 a duniya.
Sannan kuma mutum sama da milyan 1 ne cutar ta kama a duniya, cikin kwanaki kasa da 5 a fadin duniya.
Wannan ya nuna yadda annobar Korona ke kara fantsama. Sai dai kuma ana ganin yawan gwajin da ake yi ne ke kara bayyana yawan masu dauke da cutar a duniya.
A ranar Lahadi da ta gabata, yawan masu dauke da cutar a duniya ya haura milyan 20.
Amma ya zuwa Alhamis din nan kuma sun haura milyan 21 a duniya.
Runbun adana adadin kididdigar masu dauke da cutar Coronavirus, worldometer.info, ya kididdige cewa tsawon kwanakin nan hudu a jere, a kullum ana samun sama da mutum 200,000 sun kamu da cutar a duniya.
Yawan Mace-mace: Korona ta kashe sama da mutum 50, 000 cikin kasa da kwanaki 5 a duniya, daga ranar Lahadi zuwa ranar Alhamis din jiya.
Korona ta kashe sama da jimillar murum 750,000 a duniya. Cutar ta fi yin mummunan kamari a Amurka, Rasha sai kuma Brazil.
Gwajin Korona A Saukake: Yawaita da saukake gwajin cutar Korona musamman a Amurka ya sa ana ganin cewa yanzu a duniya, Allah kadai ya san iyakar wadanda ke dauke da cutar a duniya.
Amurka mai yawan jama’a milyan 300, an yi wa milyan 70 gwaji. Najeriya mai jama’a sama da milyan 200, ta yi wa mutum 340,000 kacal gwaji.
Mutum milyan 5.4 suka kamu da Korona a Amurka. Milyan 3.2 a Brazil, sai milyan 2.4 a Indiya.
Zuwa ranar Alhamis mutum 21,099,879 suka kamu da cutar a duniya.