Korona ta kori Shoprite daga Najeriya

0

Katafaren kantin zamani mallakar ‘yan Afrika ta Kudu da ke da reshe a Najeriya, Shoprite, ya bayyana sanarwar shirye-shiryen ficewa daga Najeriya ba da dadewa ba.

Hadadden Rukunin Kantunan Shoprite, Shoprite Holding Limited ne ya yi wannan sanarwa a safiyar Litinin, inda ya ce sun dauki wannan mataki ne tun bayan nazarin da suka yi na jimillar cinikin karshen shekara a ranar 28 Ga Yuni, 2020.

Shoprite, wanda katafaren kantin zamani ne da ke da rassa a kasashen duniya, ya ce duk da killace jama’a da aka yi a Najeriya saboda Coronavirus, cinikin su ya karu da kashi 6.4% a wannan shekara, wato kudin Afrika ta Kudu R156.9.

Sai dai sun ce lura da masu bukatar da ke son sayen kadarorin su ne ya sa za su janye daga Najeriya, kamar yadda za su tashi daga wasu kasashe na Afrika.

Sai dai kuma sun ce duk da cewa cinikin da ake yi a Najeriya bai ragu ba, kamar yadda ake yi kafin cutar Coronavirus, to shi kan sa cinikin ba wani abin a zo a gani ba ne.

“Za mu sayar da komai mu tarkata na mu mu bar Najeriya. Saboda a Najeriya mu na da kantama-kantaman kantina 26 a jihohi 8 har da Abuja. Sannan mu na da wasu kantinan a wasu kasashen Afrika ta Kudu. Amma gaba dayan cinikin da aka yi a Najeriya da sauran kasashen Afrika, bai fi kashi 11.6 na gaba dayan cinikin da Shoprite ya yi a Afrika ta Kudu kadai ba.”

Sun bayyana sakwarkwacewar cinikin su a kantinan su da ke kasashen Afrika da sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus, wadda ta haddasa: “killace jama’a cikin gida, rufe kantuna a duniya, nesantar juna yayin mu’amaloli, takaita zirga-zirgar jirage da motoci, takaita zirga-zirgar jama’a, takaita lokutan bude kantina, takaita ma’aikata da sauran su.”

Shoprite sun buge kantin farko a Najeriya cikin Disamba, 2005. Amma yanzu su na da kantina 26 a cikin jihohi 8 har da Abuja.

Cikin sanarwar su ta fara shirin barin Najeriya, Shoprite ya ce ya dauki ‘yan Najeriya har sama da 2,000. Kuma ya gina kyakkyawar mu’amalar kasuwanci da dillalan kayan masarufi, manya da kananan masu hada-hadada kuma manoma sama da 300.

Share.

game da Author