KORONA: Shagon magani a Najeriya na saida fakitin maganin ‘Hydroxycholroquine’ naira 50,000

0

Wani shagon magani dake garin Fatakwal jihar Ribas na saida fakitin kwayoyin magani na Hydroxychloroquine naira 50,000.

Maganin da ada ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin cizon sauro wanda har hukumar lafiya ta duniya ta dakatar da yin amfani da shi saboda ya daina aiki a jikin mutane amma bayan barkewar annobar Korona sai kuma aka rika bayyana cewa yana maganin cutar.

Tun daga wannan lokaci, maganin ya fara dan karan tsada da har ya kai naira 50,000 kamar yadda wannan shago ke saida wa a Fatakwal.

Ganin tsadar kudin wannan maganine ya sa wasu da suka dauki hoton kwalin maganin suka yada a shafukan yanar gizo inda.

Ko da aka tambayi ko menene dalilin tsadar wannan magani daga bakin masu wannan shago sai suka ce suma sun siyo maganin da tsadar gaske ne shine ya sa aka ga haka.

” Da kuke cewa wannan magani yayi dan karan tsada, kun nemi sanin nawa ake saida maganin a manyan kantinan saida magani a Legas, Abuja da wasu jihohin kunji.

” Tun lokacin da annobar Korona ta karade duniya, magungunan da ake amfani da su wajen warkar da cutar suka yi tashin gwauron zabi.

Farashin kwayoyin magani na Bitamin C da Zinc sun tashi matuka.

Wakilin PREMIUM TIMES da ya zazzagaya wasu wuraren ya gano cewa lallai akwai wasu shagunan da ke sai da maganin da dankaran tsada.

Wasu har naira 75,000 suka saida maganin Hydroxychloroquine, a kasar nan.

Ita dai wannan magani ko hukumar Lafiya ta WHO ta tabbatar da rashin ingancinta wajen warkar da Korona, sai dai kuma duk da haka ita ce dai maganin da ake dirka wa wanda ya kamu da cutar domin samun lafiya.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar a jihar cewa a rika amfani da wannan magani domin warkar da duk wanda ya kamu da cutar Korona a jihar.

” Ni ma ita aka yi ta bani har na warke. Saboda haka a rika amfani da ita.” Inji gwamna Bala.

Share.

game da Author