KORONA: Najeriya ta zarce mutum 53,000 da suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 221 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –17, Filato-60, FCT-33, Kaduna-26, Rivers-18, Enugu-9, Kwara-9, Ondo-9, Nasarawa-6, Gombe-5, Anambra-5, Delta-4, Abia-4, Imo-3, Edo-2, Ogun-2, Oyo-2, Osun-2, Bauchi-1 da Kano-1

Yanzu mutum 53,021 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 40,281 sun warke, 1,010 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,730 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,035 FCT –5,079, Oyo – 3,060, Edo –2,555, Delta –1,719, Rivers 2,108, Kano –1,722, Ogun – 1,633, Kaduna –2,085, Katsina –771, Ondo –1,524, Borno –740, Gombe – 719, Bauchi – 645, Ebonyi – 965, Filato -2,245, Enugu – 1,096, Abia – 759, Imo – 526, Jigawa – 322, Kwara – 945, Bayelsa – 378, Nasarawa – 427, Osun – 771, Sokoto – 156, Niger – 239, Akwa Ibom – 271, Benue – 451, Adamawa – 217, Anambra – 207, Kebbi – 92, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 238, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.

Mutanen da yunwa za ta kashe a Afrika za su haura wadanda Coronavirus ta kashe -IFAD

Cibiyar Bunkasa Harkokin Noma ta Duniya (IFAD), ta bayyana cewa akwai wasu karin akalla mutane milyan 23 da yunwa za ta kassara a Kasashen Yankin Saharar Afrika, a cikin shekarar 2020.

Shugaban IFAD Gilbert Houngbo ne ya bayyana haka a wurin taron Zauren Tattauna Tattalin Arziki, na World Economic Forum.

Taron na bana an tattauna matsalar Hanyoyin Tattalin Abinci A Afrika, a lokacin annobar Coronavirus.

Houngbo ya ce nazari, hasashe da kirdadon yadda ake fuskantar matsalar abinci, ya nuna cewa a shekarar 2020 wadanda yunwa za ta kashe a yankin Afrika za su zarce wadanda cutar Coronavirus ta kashe, nesa ba kusa ba.

IFAD dai cibiya ce wadda ta shahara wajen tallafa wa mutanen da ke zaune a karkara wajen bunkasa noma, kara samar wa ‘ya’yan su abinci mai gina jiki da kuma samar wa kan su kudaden shiga ta hanyar noma.

Houngbo ya ce Coronavirus ta nuna cewa akwai hagarimar matsalar tsarin samar da abinci, raba shi da kuma gyarawa.

Manoma da dama na kokawa da yadda ba su iya samun taking zamani saboda dokar hana zirga-zirga.

Sannan kuma ba su iya zuwa gona kuma wadanda suka noma amfanin gona na sayarwa, an rufe kasuwanni ballantana su rika sayar da amfanin gonar su.

Rahoton ya kara da cewa a shekarar 2019 yunwa ta kassara mutum milyan 135 a duniya, wadanda milyan 73 daga cikin su sun fito daga Afrika, cikin kasashe 36.

A Arewacin Najeriya yunwa ta kassara mutum milyan 5 a 2019.

Share.

game da Author