KORONA: Mutum 457 suka kamu ranar Laraba, 17 sun rasu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 457 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -137, FCT-76, Plateau-40, Rivers-35, Enugu-34, Oyo-25, Abia-23, Delta-12, Edo-11, Ebonyi-11, Cross River-10, Kwara-10, Kaduna-9, Anambra-7, Ogun-5, Imo-3, Bauchi-3, Osun-2, Nasarawa-2, Kano-1 da Ekiti-1

Yanzu mutum 44,890 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 32,165 sun warke, 927 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,798 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,551 FCT – 4,163, Oyo – 2,807, Edo – 2,328, Delta –1,541, Rivers 1,894, Kano –1,599 , Ogun – 1,416, Kaduna – 1,507, Katsina –746, Ondo – 1,243 , Borno –628, Gombe – 620, Bauchi – 568, Ebonyi – 880, Filato – 1,283, Enugu – 819, Abia – 625, Imo – 472, Jigawa – 322, Kwara – 800, Bayelsa – 342, Nasarawa – 343, Osun – 586, Sokoto – 153, Niger – 226, Akwa Ibom – 221, Benue – 356, Adamawa – 176, Anambra – 142, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 153, Taraba- 72, Kogi – 5, da Cross Rivers – 68.

Rahoton watan Agusta da Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta first ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ba su da wata mu’amala da kusanci da wanda ya fita kasar waje, ko wata jiha ko kusanci da mai cutar Coronavirus.

Hakan ya na nufin akasarin wadanda suka kamu a Najeriya, ba su san ta yadda aka yi suka kamu ba.

Duk da raguwar yawan rahotannin adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke yi a kullum a yanzu, har yau akwai fargabar cewa sake bude harkokin komai a kasar nan a yanzu zai iya zama sammakon-bubukuwa.

Share.

game da Author