KORONA: Mutum 437 suka kamu ranar Lahadi, 3 sun rasu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 437 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –107, FCT-91, Filato-81, Kaduna-32, Ogun-30, Kwara-24, Ebonyi-19, Ekiti-17, Oyo-8, Borno-6, Edo-6, Kano-4, Nasarawa-3, Osun-3, Taraba-3, Gombe-2 da Bauchi-1.

Yanzu mutum 46,577 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 33,186 sun warke, 945 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,446 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,875 FCT – 4,467, Oyo – 2,868, Edo – 2,382, Delta –1,596, Rivers 1,939, Kano –1,626, Ogun – 1,469, Kaduna – 1,598, Katsina –746, Ondo –1,284 , Borno –688, Gombe – 631, Bauchi – 577 , Ebonyi – 870, Filato -1,502, Enugu – 905, Abia – 644, Imo – 476, Jigawa – 322, Kwara – 852, Bayelsa – 346, Nasarawa – 370, Osun – 628, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 235, Benue – 409, Adamawa – 185, Anambra – 142, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 178, Taraba- 75, Kogi – 5, da Cross Rivers – 68.

Gwajin maganin rigakafin cutar covid-19 na Rasha na matakin karshe.

Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Rasha Oleg Grinev ya bayyana cewa maganin rigakafin Korona da kasar ta hada na matakin gwaji na karshe kafin fara amfani da shi.

Grinev ya ce gwamnati na kokarin yi wa maganin rajista cikin mako mai zuwa.

” Ina tabbatar da cewa maganin warkar da cutar Korona na da ingancin warkar da cutar a jikin mutum.

Wani cikin masana kimiyya da suka hada maganin ya ce suna sa ran fara sarrafa maganin da yawa a watan Satumba.

Hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Research Institute for Epidemiology and Microbiology’ ce ta hada wannan magani.

Hukumar ta gwada inganci da sahihancin aikin maganin a jikin wasu ma’aikatan gwamnati da sojoji.

Sakamakon gwajin ya nuna cewa rigakafin ya warkar da cutar a jikin wadannan mutane ba tare da sun Samu matsaloli ba.

Share.

game da Author