Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 373 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 69, Osun-41, Kaduna-40, Oyo-40, FCT-35, Filato-22, Rivers-19, Kano-17, Ondo-17, Ogun-15, Abia-14, Gombe-12, Imo-9 Enugu-7, Kwara-6, Delta-5, Niger-2, Borno-1, Bauchi-1 da Nasarawa-1
Yanzu mutum 48,116 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 34,309 sun warke, 966 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,841 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 16,256 FCT – 4,632, Oyo – 2,935, Edo – 2,399, Delta –1,626, Rivers 1,991, Kano –1,661, Ogun – 1,521, Kaduna – 1,706, Katsina –746, Ondo –1,373 , Borno –698, Gombe – 647, Bauchi – 580, Ebonyi – 908, Filato -1,665, Enugu – 976, Abia – 677, Imo – 494, Jigawa – 322, Kwara – 888, Bayelsa – 346, Nasarawa – 372, Osun – 719, Sokoto – 154, Niger – 228, Akwa Ibom – 241, Benue – 430, Adamawa – 185, Anambra – 156, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 194, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 73.
Gwamnati zata siyo na’urorin gwajin KORONA na naira biliyan 8.49
Ganin yadda cutar KORONA ke dada yaduwa a kasar nan gwamnati ta ware naira biliyan 8.49 domin siyo kayan yin gwajin cutar a kasar nan.
A jawabin da ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare yayi a wajen taron majalisar zartaswa ta Kasa ranar laraba, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda cutar ke dada yaduwa a Najeriya.
Ya ce siyo wadannan na’urori zai taimaka wajen aikin dakile yaduwar annobar Korona a duniya.
Osagie ya ce hukumar NCDC za ta bude sabbin wurare yin gwajin Korona a duk kananan hukumomin dake kasar nan domin dakile yaduwar cutar.
Sakamakon gwajin cutar covid-19 da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna an samu karin mutum 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Discussion about this post