Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 250 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –21, Filato-69, FCT-41, Delta-14, Kaduna-14, Bayelsa-13, Enugu-13, Ekiti-11, Bauchi-9, Ogun-8, Edo-7, Oyo-7, Rivers-6, Adamawa-4, Osun-4, Nasarawa-3, Ebonyi-2, Kwara-2, Gombe-1 da Imo-1
Yanzu mutum 53,727 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,314 sun warke, 1,011 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,402 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,040, FCT –5,149, Oyo – 3,107, Edo –2,577, Delta –1,744, Rivers 2,134, Kano –1,725, Ogun – 1,646, Kaduna –2,114, Katsina –789, Ondo –1,534, Borno –740, Gombe – 723, Bauchi – 666, Ebonyi – 973, Filato -2,443, Enugu – 1,155, Abia – 763, Imo – 527, Jigawa – 322, Kwara – 958, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 779, Sokoto – 158, Niger – 241, Akwa Ibom – 278, Benue – 451, Adamawa – 221, Anambra – 207, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 262, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.