KORONA: Mutum 160 wun kamu ranar Juma’a, Yanzu mutum 53,477 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 160 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 27, Filato-44, Katsina-18, Edo-15, FCT-14, Ondo-10, Oyo-9, Kwara-6, Abia-4, Nasarawa-4, Kano-3, Ekiti-2, Kaduna-2, Kebbi-1 da Ogun-1

Yanzu mutum 53,477 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,017 sun warke, 1,011 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,449 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,083 FCT –5,108, Oyo – 3,100, Edo –2,570, Delta –1,730, Rivers 2,128, Kano –1,7225, Ogun – 1,638, Kaduna –2,100, Katsina –789, Ondo –1,534, Borno –740, Gombe – 722, Bauchi – 657, Ebonyi – 971, Filato -2,374, Enugu – 1,142, Abia – 763, Imo – 526, Jigawa – 322, Kwara – 956, Bayelsa – 378, Nasarawa – 431, Osun – 775, Sokoto – 158, Niger – 241, Akwa Ibom – 278, Benue – 451, Adamawa – 217, Anambra – 207, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 251, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.

NAFDAC bata kammala yin gwajin Ingancin maganin gargajiya ba da aka hada a Najeriya ba

A yayin da ƙasashen Turai ke cigaba da yin gwaje-gwaje ingancin maganin Korona da suka hada, Najeriya ma ba a barta a baya ba wajen hadawa da yin nata gwajin magungunan.

Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa tana yun gwajin magungunan warkar da Korona har guda 40 da masu hada magungunan gargajiya suna mika wa hukumar.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta sanar da haka tana mai cewa ana yin gwajin ingancin magungunan ne saboda kada wajen neman kiba a samo rama.

“Tun bayan bayyanar annobar Korona, masu hada maganin gargajiya suka fantsama bincike domin ganin suma ba a barsu a baya ba wajen ganin an hada maganin cutar. Da yawa cikin su sun mika samfarin maganin su ga hukuma domin yin gwaji da tantance ingancin sa.

” Haka kuma NAFDAC ta gindaya musu wasu sharudda da dokoki da za su bi wajen hada maganin.

“Za a yi gwajin ingancin magungunan a dabbobi a karon farko tukunna.

Mojisola ta gargadi masu maganin kada su kuskura su jaraba wani magani ba tare da hukumar ta bada daman haka ba.

Share.

game da Author