Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 304 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –81, FCT-39, Abia-31, Kaduna-24, Rivers-23, Filato-16, Cross River-13, Ebonyi-12, Ondo-12, Ekiti-11, Edo-11, Benue-10, Nasarawa-10, Ogun-6 da Gombe-5.
Yanzu mutum 43,841 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 20,308 sun warke, 888 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,645 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,267 FCT – 3,972, Oyo – 2,768, Edo – 2,311, Delta – 1,510, Rivers 1,829, Kano –1,597 , Ogun – 1,403, Kaduna – 1,481, Katsina –745, Ondo – 1,204 , Borno –613, Gombe – 612, Bauchi – 560, Ebonyi – 808, Filato – 1,221, Enugu – 821, Abia – 582, Imo – 469, Jigawa – 322, Kwara – 753, Bayelsa – 339, Nasarawa – 339, Osun – 553, Sokoto – 153, Niger – 224, Akwa Ibom – 221, Benue – 356, Adamawa – 164, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 152, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 58.
KIRA GA MATASA: Cutar Korona har kisa ta na yi idan ta Kama matashi – Shugaban WHO
Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus ya gargadi matasa da ke cewa kwayoyin cutar Korona ba zai iya kama su ba da su daina wannan zato, yana mai cewa ba kama matashi ba ma kawai har kisan sa zai iya yi idan bai kiyaye ba.
Bayan haka kuma ya shaida cewa lokaci yayi da kasashen duniya za su koyi shirin zama dindindin da kwayoyin cutar Korona.
Dole ne mu koyi rayuwa da wannan cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da sauran jama’a.
Sannan kuma ya yabawa kasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.
Discussion about this post