Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 329 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –113, Kaduna-49, FCT-33, Filato-24, Kano-16, Edo-15, Ogun-14, Delta-13, Osun-10, Oyo-8, Ekiti-6, Bayelsa-6, Akwa Ibom-5, Borno-4, Enugu-4, Ebonyi-3, Rivers-2, Bauchi-1, Nasarawa-1, Gombe-1 da Niger-1
Yanzu mutum 48,445 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 35,998 sun warke, 973 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,474 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 16,369 FCT – 4,665, Oyo – 2,943, Edo – 2,414, Delta –1,639, Rivers 1,993, Kano –1,677, Ogun – 1,535, Kaduna – 1,755, Katsina –746, Ondo –1,373 , Borno –702, Gombe – 648, Bauchi – 581, Ebonyi – 911, Filato -1,689, Enugu – 980, Abia – 677, Imo – 494, Jigawa – 322, Kwara – 888, Bayelsa – 346, Nasarawa – 373, Osun – 729, Sokoto – 154, Niger – 229, Akwa Ibom – 246, Benue – 430, Adamawa – 185, Anambra – 156, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 200, Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 73.
Maganin Korona da Rasha ta hada zai yi aiki a jikin masu shekaru 18 zuwa 60 ne.
Idan ba a manta ba a wannan mako ne babban Jami’i a sashen masana kimiyyar magunguna na ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Rasha Vladimir Bondarev ya bayyana cewa maganin rigakafin Korona da kasar Rasha ta hada zai fi tasiri ne akan wadanda shekarun su bai wuce daga 18 – 60 ba.
Bondarev ya fadi haka a taron manema labarai da aka yi a Moscow, babban birnin kasar Rasha ranar Laraba.
Ya ce masana kimiyya za su cigaba da gudanar da bincike domin ganin maganin ya yi wa mutanen da suka dara shekaru 60 aiki.
“Bisa ka’ida duk maganin da za a hada a kasar Rasha za a tabbatar cewa zai yi wa jarirai zuwa masu shekaru fiye da 60 aiki a jiki ba tare da sun samu matsaloli ba.
“Sai dai wannan karon masana kimiyyar magunguna sun gwada inganci da sahihancin maganin rigakafin Korona a jikin mutane masu shekaru 18 zuwa 60 ne kuma suka gano rigakaifin zai fi yi wa wadanda ke da shekaru 18-60 ne tasiri.
Daya daga cikin masanan da suka hada maganin Alexander Gintsburg ya dara shekaru 60 kuma ya yi amfani da maganin bayan an hada.
Gintsburg ya ce tun bayan ya sha yaji jikin sa garau, babu wata matsala.
Maganin rigakafin da aka hada iri biyu ne da ake hadawa a yi wa mutum alluran su. Maganin zai karawa garkuwar jikin mutum karfi sannan ya warkar da mara lafiya.