KORONA: Jihar Filato ce ke kan gaba a alkaluman ranar Juma’a, mutum 103 suka kamu, sai Abuja

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 443 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 70, Filato-103, FCT-60, Ondo-35
Edo-27, Rivers-27, Kaduna-20, Osun-19, Borno-18, Oyo-18, Kwara-11, Adamawa-9, Nasarawa-7, Gombe-6, Bayelsa-4, Imo-4, Bauchi-2, Ogun-2 da Kano-1.

Yanzu mutum 45,687 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 32,637 sun warke, 936 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,114 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,697 FCT – 4,301, Oyo – 2,843, Edo – 2,367, Delta –1,557, Rivers 1,938, Kano –1,609 , Ogun – 1,430, Kaduna – 1,550, Katsina –746, Ondo – 1,243 , Borno –652, Gombe – 626, Bauchi – 576, Ebonyi – 838, Filato –1,397, Enugu – 880, Abia – 625, Imo – 476, Jigawa – 322, Kwara – 826, Bayelsa – 346, Nasarawa – 367, Osun – 605, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 324, Benue – 356, Adamawa – 185, Anambra – 142, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 159, Taraba- 72, Kogi – 5, da Cross Rivers – 68.

Share.

game da Author