KORONA: Har yau babu ranar komawa makarantu a Najeriya – Ministan Ilmi

0

Karamin Ministan Ilmi, Chukwuemeka Nwsjiuba, ya bayyana cewa har yau har gobe gwamnatin tarayya ba ta sa ranar da dalibai za su koma makaranta gaba daya ba.

Sai dai kuma karamin ministan ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren ilmi domin kokarin bayyana lokacin da ake ganin ya fi dacewa a koma makarantun.

Ministan ya yi wannan bayanin ne yayin ganawa da manema labarai da Kwamitin Shugaban Kasa na Dakile Cutar Coronavirus ya yi da manema labarai a ranar Litinin.

Amma ya bayyana cewa ya na da yakinin cewa ranar komawa makarantun ns nan kusa, ba da dadewa ba. “Amma dai duk da hakan, ba za mu fito fili mu rika cewa saura kwana kaza, ko ranar kaza ga watan kaza za a sake bude makarantun gaba daya ba.”

An kulle dukkan makarantun Najeriya watanni biyar da suka gabata, saboda barkewar cutar Coronavirus, wadda zuwa yanzu ta kashe sama da mutum 1,000 a Najeriya.

Sai dai kuma daliban da ke kan zangon karshe na fita makarantu, wato ‘yan JSS3 da SSS3, sun koma makaranta su na rubuta jarabawar fita.

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa komawar daliban da za su rubuta jarabawa alama ce da ke nuna sauran daliban ma ya kamata su koma.

Sai dai kuma bayanin Ministan Ilmi ya nuna har yanzu gwamnatin tarayya ba ta kammala shirin komawar sauran daliban zuwa makarantu ba.

Jami’o’i Da Sauran Manyan Makarantu:

A ranar Litinin din dai Minista ya yi magana a kan manyan makarantun gaba da sakandare, inda ya ce Babban Minstan Ilmi, Adamu Adamu ya gana da masu ruwa da tsaki a ranar Litinin din da rana, dangane da batun komawa makaranta.

“Jami’o’i 78 masu zaman kan su sun shaida wa Minista Adamu cewa a shirye suke su koma makaranta su da dukkan daliban su. Amma makarantun gwamnati kuma har yanzu kimtsawar ta su rabi-da-rabi ce.”

Ya ce bayan an gama tattaunawa an cimma matsayar kammala shirye-shiryen komawa makarantun, to zai sake dawowa ga Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Cutar Coronavirus ya sanar da ranar da za a koma dukkan makarantun kasar nan baki daya.

Ministan ya kara bada hakuri ga dalibai masu zanga-zangar neman a bude musu jami’o’i domin su koma karatu, cewa su dan kara hakuri zuwa nan ba da dadewa ba.

Sai dai kuma a halin da ake ciki, ko da gwamnatin tarayya ta bayyana ranar komawa makarantu, to ba za a bude akasarin jami’o’in gwamnati ba, saboda malaman jami’o’i sun shiga yajin aiki.

Share.

game da Author