Gwamnatin tarayya ta umurci ma’aikatan gwamnati dake mataki na 12 zuwa 13 su Koma aiki.
Shugaban ma’aikata, Folashade Yemi-Esan ta karanta sanarwar ranar Litini a Abuja.
A yanzu ma’aikata daga mataki na 14 zuwa sama da ma’aikatan bada agajin gaggawa ne ke zuwa aiki sau uku a mako.
Folashade ta ce bisa ga umurnin da gwamnati ta bada ma’aikatan dake mataki na 12 zuwa 13 za su Fara zuwa aiki daga ranar Litini zuwa Juma’a daga karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.
Gwamnati ta sanar da haka bayan kwamitin Shugaban kasan Kan yaki da cutar Korona ta amince ma’aikata su dawo aiki.
Kwamitin ta ce dole ma’aikata su kiyaye sharuddan kiyayewa daga kamuwa da cutar covid-19 yayin da suke aiki.
Folashade ta ce shugabannin ma’aikatu za su tabbata ma’aikata sun kiyaye dokokin Korona sannan za su iya raba musu aiki a ranaku da bamdabam domin a rage cinkoso.
Idan ba a manta ba a watan Maris ne gwamnati ta umurci ma’aikata daga rukunin 13 zuwa kasa su zauna a gida domin rage cinkoson mutane a wuraren aiki.
Sai kuma gwamnati ta ce kada jami’an kula da lafiya, ma’aikatan kwasar shara, jami’an kashe gibara da sauran masu ayyukan agajin gaggawa su zauna a gida.
Gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin rage yaduwar cutar covid-19 a kasar nan.
Ma’aikata za su ci gaba da aikin su ne idan cutar ta nuna raguwa sosai.